Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), ta bai wa sabon zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke shaidar lashe zaben jihar da aka gudanar a makon da ya gabata.
INEC ta bai wa Sanata Adeleke shaidar ne a garin Osogbo da ke a jihar ta Osun.
- Kotu Ta Karbi Dala 61,400 Da Aka Danganta Su Da Abba Kyari A Matsayin Sheda
- Sojoji Sun Sake Ceto Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok A Borno
Adeleke ya zama zakara ne a inuwar jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Osun.
Talla
Ya samu kuri’u 403,371 bayan ya kayar da abokin takararsa gwaman jihar mai ci, Gboyega Oyetola inda ahi kuma ya samu kuri’u 375,027.
Talla