An yi bikin mika jami’ar sufuri ta tarayyar Najeriya a birnin Abuja na kasar a ranar Juma’a da ta gabata, da nufin kaddamar da wannan jami’a da kamfanin CCECC dake karkashin kamfanin CRCC na kasar Sin ya zuba jari gami da ginawa.
Jami’ar, wadda ke da mazauni a garin Daura na jihar Katsina ita ce irinta na farko a duk fadin nahiyar Afirka. An fara gina bangare na farko na jami’ar ne a shekarar 2021, sa’an nan aka kammala aikin ginawa a shekarar 2022, daga baya kuma, aka gudanar da ayyukan sanya na’urorin a cikin gine-gine, da neman izinin aiwatar da aikin koyarwa.
- Tsohon Firaministan Faransa: Duniya Na Hasashen Kyakkyawar Makoma Ga Kasar Sin
- Huawei Zai Tallafa Wa Ci Gaban Fasahar Nijeriya Ta Hanyar Zuba Dala Miliyan 15 Duk Shekara
An ce, wannan jami’a za ta taimakawa kokarin kasar na raya aikin sufuri da jigilar kayayyaki, gami da tattalin arzikinta, ta hanyar samar da dimbin kwararru masu ilimi a bangaren sufuri, da na gina layin dogo.
Da yake gabatar da jawabi yayin bikin mika jami’ar, ministan kula da sufuri na tarayyar Najeriya Sa’idu Ahmed Alkali ya godewa kamfanin Sin da ya zuba jari gami da daukar nauyin gina wannan jami’a, inda ya ce kamfanin ya samar da muhimmiyar gudunmowa ga yunkurin kasar Najeriya na raya aikin ilimi. (Bello Wang)