A yau Lahadi, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na kasa da kasa, Thomas Bach, ya ziyarci tashar watsa labarai na kasa da kasa na Shanghai, na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, inda ya baiwa tawagar watsa gasar wasannin Olympics ta Paris kai tsaye ta CMG shaidar izini.
Yayin bayar da shaidar, shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana cewa, CMG za ta ba masu kallo na kasa da kasa mamaki, domin za ta gabatar da gasar wasannin Olympics mai kyau bisa matsayin samarwa da watsa shirye-shirye dake kan gaba a duniya.
A nasa jawabi, Bach ya ce, yana farin cikin ganin sabuwar hanyar da CMG ta kawo wa aikin watsa gasar wasannin Olympics kai tsaye bisa ingantattun fasahohinta, yana fatan sabbin fasahohin CMG kamar fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama, za su gabatar da sabbin abubuwa ga masu kallon gasar wasannin Olympics.(Safiyah Ma)