Hafsan hafsoshin sojojin Iran, Manjo Janar Mohammad Hossein Bagheri, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan abin da ya janyo hatsarin jirgin saman da ya janyo mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da ministansa, Hossein Amir-Abdollahian.
Kamfanin dillancin labaran kasar, IRNA ne, ya ruwaito cewa, tawaga karkashin Birigediya Janar Pilot Ali Abdollahi, da ta kunshi kwararru na kasar da kuma na soji sun isa wurin da hatsarin ya faru a gabashin Azerbaijan, kuma tuni har sun fara gudanar da bincike.
- Wang Yi: A Tsaya Kan Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin Mashigin Teku Na Taiwan
- Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga 2 Sun Ƙwato Bindigu 2 da Alburusai
An ruwaito labarin mutuwar manyan jami’an ne cikin tsakar daren ranar Litinin bayan sa’o’in da aka kwashe ana ta neman wajen da jirgin ya yi hatsari.
Wadanda suke cikin jirgin wanda ke komawa bayan ziyara zuwa Arewa Maso Yammacin iyakar kasar da Azerbaijan sun hada da gwamnan gabashin Azerbaijan, Janar Malek Rahmati da kuma wakilin jagoran addini na Iran a lardin, Ayatollah Mohammad Ali Al-e Hashem.
Kamfanin dillancin labaran na Iran, ya ce nan gaba za a bayyana sakamakon binciken.
Tuni al’ummar duniya suka shiga alhinin rasuwar Shugaba Raisi.