Gwamna Abba Kabir Yusuf, na shirin rattaba hannu kan dokar majalisar masarautu da aka yi wa kwaskwarima yayin da majalisar dokokin Jihar Kano ke ci gaba da zama a yau domin kammala dokar.
Tun a jiya ne dai jami’an tsaro suka warwatsu a duk muhimman wurare na zauren majalisar lokacin da ƙudirin dokar da ke da nufin soke kafa masarautu biyar ya tsallake karatu na farko.
- Sanata Barau Jibrin Ya Ƙaddamar Da Motocin Zirga-Zirga A Kano
- Majalisar Dokokin Kano Za Ta Yi Wa Dokar Da Ta Tsige Sarki Sanusi II Kwaskwarima
Shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne, ya fara miƙa buƙatar yi wa dokar masarautun Kano (gyara mai lamba 2) ta 2024, manyan sauyin da ake niyyar yi zai jirkita tsarin masarautun da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a shekarar 2019.
Tsohuwar dokar ta 2019 wacce ta samar da sabbin masarautun Bichi da Rano da Gaya da Ƙaraye tare da (birnin) Kano, an yi gyare-gyare da dama a cikinta, inda aka yi kwaskwarima a baya-bayan nan a shekarar 2020 da kuma 2023.
Sashe na 3(1) na dokar ya zayyana ikon waɗannan masarautun, inda kowannensu ke da ƙananan hukumomi da dama a ƙarƙashinsu.
Garan da aka yi a shekarar 2020 biyo bayan sauke Sarki Muhammadu Sanusi II, inda aka sake fasalin majalisar ta zama Sarkin Kano a matsayin mai jan ragamar na dindindin ga ragowar masarautun.
Har ila yau, dokar ta bai wa gwamna, idan har majalisar Sarakunan ta amince, ya iya tsigewa ko naÉ—a sabon Sarkin a duk masarautun.
Yanzu haka dai garin Kano yayi jim a daidai lokacin da majalisar ke shirin yin zama na musamman domin amincewa da gyaran.
Daily Trust ta rawaito cewa; wani babban jami’i a majalisar dokokin ya jaddada cewa babu wani da zai iya dakatar da yin gyaran domin sun ƙuduri niyyar yin shi tuntuni, wanda hakan ke nuni da cewa an daɗe ana shirin yin garambawul ga tsarin masarautun.
Sai dai shugaban marasa rinjaye Abdul Labaran Madari, ya tabbatar da cewa duk da cewa ƴaƴan jam’iyyar APC ba sa adawa da gyaran da aka yi niyyar aiwatarwa, amma sun dage cewa ba za a rusa ko ɗaya daga cikin masarautu biyar ɗin ba, kuma Sarkin (birnin) Kano na yanzu, Aminu Ado Bayero shi zai ci gaba da zama a kan kujerarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin Kano da Sarkin Bichi duk ba sa gari, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan illar rashin nasu.
Majiyoyi na nuni da cewa da zarar majalisar ta zartar da ƙudirin, nan take Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sanya mata hannu, wanda hakan wataƙila zai iya maido da Sarki Sanusi II.