Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai yi gaggawar rattaba hannu kan kowanne hukunci kotu ta yanke wa wanda ya kone mutane a garin Larabar Abasawa ana tsaka da sallar Asuba.
Gwamna Abba na wannan bayani ne a loakcin da ya ziyarci asibitin kwararru na Murtala da ke Jihar Kano, inda ya yi Allah wadarai da wannan mummunan abin da matashin ya aikata.
- Tinubu Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyalan Waɗanda Suka Ƙone A Gobarar Masallaci A Kano
- An Fara Shirin Jana’izar Marigayi Raisi A Iran
Ya ce lallai gwamnatinsa ba za ta bar wannan lamari haka ba, inda ya ce wannan hauka ne na karshe kuma rashin imani ne. Ya ce sun sami labarin cewa rigima ce da ta shafi iyali kan rabon gado, amma kuma bai kamata ka rufe kawunnanka da ‘yan’uwanka da sauran al’umma ka banka masu wuta suna sallar Asuba ba.
Gwamnan ya jaddada cewa ko shakka babu a matsayinsa na wadanda Allah ya dora wa nauyin kare lafiya da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano, ba zai taba barin wannan lamari haka ba.
Ya ce, “Na kawo ziyara domin duba wadanda suka samu kuna, wannan abu da wannan mugun mutun ya yi ba shida nasaba da ta’addanci, sannan ba shida nasaba da harkar siyasa, harkace ta cikin gida tsakanin zuriyya guda, an raba gado yana ganin kamar ba a yi masa daidai ba, maimakon bin hanyar doka, shi ne ya yanke wa kansa hukunci ya kashe bayin Allah, saboda shi kafiri ne. Na fada haka ne saboda idan mutun ba kafiri mara imani ba, ba wanda zai je ya tarar da al’ummar Musulmi suna Sallah ya zuba masu fetur ya banka masu wuta.
“Saboda haka ina tabbatar masa da cewa gwamnatina za ta tabbatar da kwato hakkin wadannan mutanen da aka cutar, wadanda suke kwance a wanann wuri da kuma wadanda suka rigamu gidan gaskiya. Sai mun tabbatar da kwato masu hakkinsu, duba da abin da doka ta ce a yi kan wanda ya kashe al’umma.”
Gwamna Abba Kabir ya kuma tabbatar da cewa ba zai jinkirta ba, duk abin da kotun shari’ar Musulunci ta yanke masa, zai rattaba hannu a kai domin tabbatar da cewa yadda suka ji wannan lamarin shi ma ya ji.