Ya zo a cikin zancen ninninka aiki a cikin wadannan kwanaki goma ruwayoyi daban-daban daga masu ruwaya mabanbanta, Tirmizi ya fitar, Ibn Maja ma haka ya fitar daga ruwayar Nahhasu bin Kuhaimin daga Kadatu daga Ibn Musayyib daga Abi Hurairaita ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce “Ba wasu kwanaki da suka fi soyuwa a wurin Allah a bauta masa daga wadannan kwanuka goma na watan Zulhajji. Azumin kowace rana ana gwada shi da Azumin shekara”. Idan ka yi Azumi daya a cikin wadannan kwanukan goma na Zulhajji kamar ka yi azumin shekara ne. Ka ga yanzu idan ka yi azumi daga daya ga Zulhajji zuwa tara ga watan (domin ba a azumi ranar sallah, haramun ne, don haka wadannan kwanukan tara ake ce musu goma, kuma ba a ramawa, mutum ba zai ce bayan sallah zai rama daya don su cika azumin ya zama goma ba, shari’a ba ta sa ka yin hakan ba. Wannan yana daga cikin abin da Allah yake cikawa, guda tara ne amma ya karbe su a matsayin goma).
Kowane azumin da aka yi a cikin wadannan ranakun, daidai yake da azumin shekara. Haka nan kowane dare na wadannan kwanakin, daidai yake da Daren Lailaitul Kadari. Yanzu Ramadan da duk falalar da Allah ya sa a ciki (duk da cewa shi farilla ne ma) amma Daren Lailatul Kadari guda daya ne a ciki. Amma wadannan kwana goman farko na Zulhajji duk da ba a fada karara cewa akwai Daren Lailatul Kadari a ciki ba, dararensu suna da wani dadin falala. Malamai sun ce “Dadin daraja bai sa ya zama ka fi mai daraja”. Khalidu bin Walidu sunansa ‘Takobin Allah’ amma kasancewarsa haka bai sa ya fi Sayyidina Abubakar a wurin Allah ba. Sayyidina Umar ba su hada hanya da Shaidan, idan Sayyidina Umar ya bi wata hanya Shaidan barin hanyar yake, amma sai ga shi Shaidan ya zo inda Manzon Allah (SAW) yake har ya kama shi, to ka ga a nan ai babu wanda zai ce Sayyidina Umar ya fi Manzon Allah (a uzu billahi) don an ba shi darajar da Shaidan bai bin hanyarsa, ina zai fi wanda aka ba shi shiri’ar baki daya? Idan Shaidan ya ji ana kiran sallah, gudu yake yana ihu yana kara don kar ya ji, domin idan ya ji zai zo ranar lahira ya yi wa Ladan shaida (domin duk abin da ya ji kiran sallar Ladani zai zo ya yi masa shaida ranar Lahira). To Shaidan ba ya so ya zamo a cikin masu yi wa Ladan shaida. Amma sai ga shi idan za a tayar da sallah, Manzon Allah (SAW) yakan ce wa Sahabbai ku hada sahu, ku hada kafa don na ga Shaidan yana yawo a tsakaninku kamar dankwikuyo. A nan, ka ga Shaidan yana tsoron kiran sallah amma ba ya tsoron sallah. Wannan kuma bai sa kiran sallah ya fi sallah daraja ba. Sai dai a zancen wadannan kwana goman na farkon Zulhajji kuwa, da darajar da falalar duk sun fi sauran kwanakin da ba su ba, sai dai abin da shari’a ta zo da shi kuma to dole haka za a bi.
- Girman Darajar Manzon Allah (SAW) Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (6)
- Girman Darajar Manzon Allah (SAW) Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (5)
Lailatul Kadari tana da girma, Mala’ika Jibirulu da Mala’iku suna sauka a cikinta suna sallama a gidajen mutane har zuwa ketowar alfijir. Amma kuma akwai wasu nau’in mutane wadanda ba sai a Lailatul Kadari ba. Mala’iku suna sauka gare su a kullum suna musu bushara cewa kar su ji tsoro, su yi musu bishara da Aljanna. Ma’ana ka ga su wadannan mutanen kamar kullum a cikin Lailatul Kadari suke. Tun da akwai wannan, ashe ba zai hana darajar da ke sauka a Lailatul Kadari ta ki sauka a cikin dararen wadannan kwanuku goma na farkon Zulhajji ba. Kuma fi’ilan an ga mazajen da irin ibadun da suke yi a cikin Daren Lailatul Kadari irin su suke yi a cikin dararen wadannan kwanukan. Ma’ana wadannan kwanukan goma masu girma ne.
Idan mutum yana da wasu ayyuka wadanda za su raunana shi wurin yin azumi, ba dole ba ne ya yi azumin a cikinsu ba, amma kuma akwai azumi guda daya wanda ya kunshi ninkin duk falalar da ke cikin kwana takwas na wadannan kwanukan, shi ne Azumin Arfa. Duk aikin da mutum yake yi; ya yi kokari ya azumci ranar Arfa, saboda duk garabasar da ake samu a cikin wadannan kwanukan guda takwas ana ninka ta sau goma ranar Arfa. Amma idan mutum yana da hali zai iya yin azumin kwanakin duka ya yi kokari ya yi, wanda kuma ba zai iya ba, ba laifi ya yi ta zikirai, ya rike salloli biyar din nan a cikin jam’i, bare masu karanta wuridan darika su rike da kyau. Mutum ya yi kokari ya samu sallar Isha’i da ta Asubahi a cikin jam’i. Ya zo a Hadisi, duk wanda ya samu sallar Isha’i da Asubahi a cikin jam’i yana da lada kamar wanda ya kwana yana sallah. Kowa ya yi kokari ya gyara farillarsa (idan ma ba zai iya hadawa da nafila ba), ko haka mutum ya tsaya Allah zai ba shi lada.
Sai dai shi wanna Nuhasu Ibn Kuhaimu da muka kawo shi a sama, masu Hadisi sun raunana shi. Tirmizi ya ce ya fada wa Bukhari wannan Hadisi kuma ga abin da masu Hadisi suka fada a kan Nuhasu, sai Bukhari ya ce masa ai ba ta hanyarsa ce kawai aka karbo Hadisin ba. An karbe shi daga Katadatu daga Sa’idu, sai dai mursali ne, an samu gibin mutum daya a tsakani. Ala ayyi halin dai ga ingatacce can (da muka kawo a karatunmu na baya).
An ruwaito kuma (daga hanyar da ita ma akwai rauni) daga Mujahid; daga Abdullahi bin Umar (RA) ya ce, “Babu wata rana da take mafi girma a wajen Allah daga ranar Juma’a (amma Juma’ar nan sai in ba ta yi karo da wadannan kwanaki goma) wanda aiki (azumi ko wani aikin alkhairi) a cikinta kowace rana Allah yana ba mutum ladan shekara irin kwanukan goman farko na Zulhajji. Abu Amril Naisaburi ya fitar a cikin littafin hikayoyinsa da sanadi daga Hamidin ya ce, na ji Ibn Sirina da Malam Katadatu suna cewa, Azumin kowace rana a cikin wadannan kwanaki goma ana ba da ladan (azumin) shekara a kansa. Irin wadannan maganganu fa, Malamai ba za su fada ba in ba sun ji daga Mai Shari’a ba ne. Lallai za a samu sun ruwaito ne daga Sahabban Manzon Allah (SAW); duk da ba su kawo sunayensu ba a nan.
Lallai ‘yan’uwa musulmi kowa ya yi kokari ya azumci wadannan kwanaki na goman farkon Zulhajji idan yana da hali, abin ba zai hana shi aikinsa ba, idan akwai uzirin da zai hana to sai a yi kokari a azumci ranar Arfa. Wanda yake filin Arfa shi ba zai yi azumi ba, amma ga wadanda ba su samu zuwa Hajji ba, Malamai sun dauki wannan azumi a matsayin wajibi a kansu, nafila ce amma mai karfi. Babban abu kuma shi ne Allah ya hana mu aikata aikin banza a cikin kwanakin, saboda Malamai sun ce kamar yadda ake ninka lada na aikin alkhairi a ciki, haka ma ake ninka zunubi idan an aikata laifi (wa iyazu billahi). Don haka, mu yo kokarin aikata alheri a koyaushe.