Kwanan baya, gwamnatoci da manyan jami’ai na kasashe da dama sun ci gaba da bayyana ra’ayinsu na bin manufar “kasar Sin kasa ce daya tak a duniya”, da kuma bin kuduri mai lamba 2758 na babban taron MDD. Suna masu cewa, yankin Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, kuma ba za a raba shi da kasar ba. Sun kuma bayyana adawa da masu neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin, da kuma wadanda suke tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, game da batun Taiwan, kasar Rasha tana goyon bayan kasar Sin kan burinta na samun dunkulewar kasar baki daya.
- Rundunar Sojojin Kasar Sin Ta Ci Gaba Da Yin Atisayen Soja a Wuraren Dake Kewayen Tsibirin Taiwan
- Wata Sabuwa: Wani Alkali Daga Amurka YA Dakatar Da Sake Nada Sarki Sanusi II
Shi kuma babban sakataren kula da harkokin kasashen waje na kwamitin tsakiyar jam’iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar Zimbabwe Simbarashe Mumbengegwi, ya bayyana cewa, batun yankin Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin, bai kamata sauran kasashen duniya su tsoma baki cikinsa ba.
Haka kuma, shugaban jam’iyyar Leadership Movement na kasar Zambiya, Richard Silumbe ya ce, kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin ya ba da jawabi na neman ‘yancin kan Taiwan, lallai akwai kasashen waje dake goya masa baya. Amma ba za su cimma mugun burinsu na neman raba yankin Taiwan daga kasar Sin ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)