An nemi al’ummar kasar nan da su tabbatar da samun canji wajen zaben mutane nagari da suke kyaurata za su ba su wakilci na gaskiya, domin a 2015 zuwa 2019 ya kamata ya zama izina ga ‘yan Nijeriya.
Malam Murtala Abdullahi ne yayi kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.
Malamin ya ci gaba da cewa duk da yunkurin talakawa na zabin mutanen da suke kyautata zaton za su cire masu kitse a wuta, sai gaba yake wanda dukkanin bangarori talaka na ji a jikinsa sakamakon raka jam’iyya daya a madafun iko.
Malamin ya yaba wa kungiyoyin da suka tashi wajen wayar da kan jama’a muhimmancin katin zabe duk da cewar har yanzu da hukumar zabe ke shirin rufewa yankin arewa na baya bisa kididdiga wajen karban katin zaben.
Malam Murtala ya ce suna da tabbacin yadda al’ummar kasar nan suka galabaita duba da abin da ya faru a zaben Jihar Osun, za a samu gagarumin canji a babban zaben 2023, amma wajibi ne kowa ya tabbatar ya mallaki katin zabe kafin lokacin, domin za a yi amfani da kudi wajen sayen kuri’a jama’a su karba kuma su yi abin da ya dace kawai.