Bayan dakatarwa ta sama da shekaru 4, a farkon wannan mako an gudanar da taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu. Kuma yayin jawabin da ya gabatar ga taron harkokin kasuwanci karo na 8 tsakanin kasashen uku, firaministan Sin Li Qiang ya bukaci kasashen su dakile duk wani kutse daga waje da zai illata dangantakarsu.
Hakika, lokacin da aka shafe ba tare da gudanar da taron kasashen 3 ba, ya nuna tsanani da kuma girman yadda wasu kasashe daga waje ke tsoma baki cikin harkokin wadannan makwabta, lamarin da za a iya cewa bai amfani yankin da komai ba sai tankiya. Kasancewar Sin da Japan da Korea ta kudu matsayin makwabta, abu ne mai muhimmanci dake tattare da dimbin damarmaki. Kasashen dake makwabtaka da juna da kamanceceniyar al’adu, na da damarmakin raya kansu cikin aminci da girmama juna, idan har suka toshe kutse daga waje. A ganina, ci gaban daya daga cikinsu, nasara ce ga dukkansu, domin abu ne da kowannensu zai iya cin gajiyarsa. Kana kyautatuwar dangantaka a tsakaninsu, ita ce za ta bunkasa musaya da fahimtar juna tsakanin jama’arsu, wanda zai kai ga samun al’ummomi masu jituwa dake zaune lafiya, kuma ’yan uwa juna.
Hadin gwiwa tsakanin bangarorin 3 shi ne zai ba su damar kara fahimtar juna da dinke duk wata baraka ko sabanin da za a iya samu a tsakaninsu. Bai kamata wasu daga cikinsu su rika barin wasu daga waje na tsoma baki cikin harkokinsu, ko jan ragamar harkokin da su ta shafa ba. Mai daki aka ce, shi ya san inda yake masa yoyo. Don haka, babu wata kasa daga waje da za ta fi su sanin yanayin da suke ciki da kuma bukatun da suke da shi, haka kuma babu wata daga waje da za ta fi su iya warware sabaninsu da kuma samar musu da hanyar raya kansu. Barin wata kasa tana hure musu kunne, tamkar tsaiko ne ga cikakken ’yancin da suke da shi a matsayinsu na kasashe.
- Mozambique: An Shirya Maido Da Noman Alkama Bisa Tallafin Fasahohin Kasar Sin
- Kotu Ta Hana Hukumomin Tsaro Tumɓuke Sarki Sanusi II
Ci gaban yankin da kwanciyar hankalinsa, ya dogara ne ga yunkurin kasashen Korea ta Kudu da Japan na kare cikakken ’yancin kansu, ta hanyar toshe duk wata kafa ta tsoma baki cikin harkokin yankin da kuma sanya muradun yankin a gaban komai. Kowa dai ya san kasar Sin kasa ce dake tabbatar da cikakken ikonta, kuma ba ’yar amshin shata ba ce, haka kuma ba ta tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe.
Fatan ita ce, kasashen Korea ta Kudu da Japan za su gyara kuskurensu, su sanya muradun al’ummominsu da na makwabtansu gaba da komai, kana su yi hadin gwiwa bisa gaskiya da girmama juna domin tabbatar da ci gaban yankin da ma kwanciyar hankalinsa.