A ranar Laraba ne tawagar dattawa 103 daga shiyyar Kano ta Kudu mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu da ta hada da Rano, Gaya da Karaye, suka bukaci a maido da masarautu biyar da gwamnatin jihar ta soke don kaucewa wariya da dakile ci gaban da al’ummar yankin suka fara dandana.
Tawagar da ta kunshi tsofaffin kwamishinoni da sauran su, sun zo ne a karkashin jagorancin tsohon kwamishina a Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, Musa Salihu Doguwa.
- Sake Shan Kaye Game Da Batun Yankin Taiwan A Wajen WHA Ya Nuna Cewa Yunkurin Ware Taiwan Daga Kasar Sin Ba Zai Yi Nasara Ba
- Tabbatar Da Cikakken ’Yancin Kai, Ita Ce Za Ta Kyautata Dangantakar Sin Da Japan Da Korea Ta Kudu
Doguwa ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi la’akari da ci gaban zamantakewa da samar da ababen more rayuwa da aka samu bayan kirkiro wadannan masarautu guda biyar da tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi.
“Mun taru ne a yau domin yin karin haske kan gagarumin ci gaba da inganta sabbin masarautu a kudancin Kano ya kawo a karkashin jagorancin tsohon Gwamna Umar Abdullahi Ganduje.
“Kara darajar Masarautun ya kawo sauyi a fagen faɗaɗa muhimman ababen more rayuwa a al’ummar da ke karkashi da kewayen Masarautar.” in ji Doguwa