Majalisar Wakilai za ta gudanar da bincike kan sallamar ma’aikata kusan 600 da Babban Bankin Nijeriya CBN ya yi daga aiki.
Kudurin ya biyo bayan aamincewa a karkashin kudirin kula da kuken jama’a da dan majalisa Jonathan Gbefwi (SDP, Nasarawa) ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.
- Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Dawo Da Tsohon Taken Nijeriya
- Majalisar Dattawa Ta Amince Da Dokar Dawo Da Tsohon Taken Kasa
Da yake gabatar da kudirin, Gbefwi ya bayyana cewa, CBN a wani bangare na wani gagarumin garambawul na rage yawan ma’aikata wanda a baya-bayan nan ya shafi ma’aikata kusan 600, ciki har da daraktoci da kusan dukkan ma’aikatan da ke ofishin Gwamnoni.
Ya ce, wannan garambawul da babban bankin ya yi, ya haifar da damuwa da cece-kuce a tsakanin masu ruwa da tsaki da suka hada da ma’aikatan da abin ya shafa da kungiyoyin kwadago da sauran jama’a.