Gwamnonin jihohin Adamawa, Benuwai, Borno da Yobe sun sha alwashin ware kaso sama da biyar daga cikin kasafin kudin jihohinsu domin taimaka wa rayuwar ‘yan gudun hijira sama da miliyan hudu da suke zaman neman mafaka a jihohinsu.
Gwamnonin sun sha alwashin ne yayin wani taron kaddamar da shiri na musamman domin nemi mafita mai dorewa kan halin da ‘yan gudun hijira ke ciki da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas Karo Na 10, Me Ya Kamata Ku Sani?
- Mun Rage Barazanar Ƴan Bindiga Da 70% A Jihar Katsina – Gwamna Radda
Da take magana a yayin taron ta yanar gizo, mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed, ta ce lalubo bakin zaren shawo kan matsalolin na ‘yan gudun hijira na daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata Nijeriya ta sanya a gaba kuma ita kanta majalisar dinkin duniya ta damu da lamarin.
Ta lura kan cewa adadin ‘yan gudun hijira ya ninku a cikin shekaru goma da ya kai kusan mutum miliyan 76 da suke halin gudun hijira a fadin duniya.
“Sama da ‘yan Nijeriya miliyan hudu na neman mafita zuwa inda aka tilasta musu yin kaura na dole,” ta ce, tsarin a matakin farko zai ba da mafita kan yadda za a nemi hanyoyin magance matsalolin da suka shafi na mutanen.
Tun da farko a jawabinsa, mukaddashin babban sakataren majalisar dinkin duniya kuma mashawarci kan nemo mafita mai dorewa, Mista Robert Piper, ya jinjina wa irin azamar gwamnatin Nijeriya da shugabanninta wajen ganin sun zama kasa ta farko a cikin kasashe 15 wajen kaddamar da shirin neman mafita mai dorewa ga ‘yan gudun hijira.
Piper ya ce kaddamar da shirin wata alama ce da ke nuni da cewa tabbas ‘yan siyasan da suke kan mulki a yanzu sun himmatu wajen ganin sun taimaka wa ‘yan gudun hijira da nema musu mafita a Nijeriya. Ya ce, dabarbaru da hikimomin yadda za a bi duk suna kunshe cikin shirin.
Shi kuma a nasa bangaren, mataimakin shugaban kasar Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ne na samar da hadin guiwa a duniyance wajen ganin an shawo kan matsalolin ‘yan gudun hijara a Nijeriya.
Ya ce, gwamnatin tarayya ta himmatu ainun wajen ganin ta kyautata da kare rayuwar ‘yan gudun hijira.
Da yake kaddamar da shirin da za a aiwatar a jihohi hudu da suke arewa Adamawa, Benuwai, Borno da Yobe, Shettima ya ce, babu yadda za a yi gwamnati ta dage idonta daga kan ‘yan gudun hijira ko daina damuwa da matsalolinsu, a maimakon hakan ya tabbatar da cewa dole ne a kare rayuwar kowani dan kasa.
Shi kuma a nasa bangaren, gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce, gwamnatin jihar a shirye take dari bisa dari wajen aiwatar da shirin da aka tsara domin nemo mafita. Ya ce, gwamnatinsa za ta iya ware kaso mai tsoka fiye da yadda ake tsammani domin nasarar shirin.
Zulum ya ce, gwamnatinsa tana kokarin yadda za su maida ‘yan gudun hijira garuruwansu na asali domin ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu.
Shi ma gwamna Jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya ce, kaddamar da shirin zai taimaka sosai wajen kyautata rayuwa da jin dadin al’umman da suke jiharsa.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ce, sun maida hankali wajen gudanar da ayyukan da kai tsaye za su kyautata da inganta rayuwar al’ummarsu, don haka a shirye suke su mara wa shirin kyautata rayuwar ‘yan gudun hijira baya.