A ranar 26 ga watan Yuni na kowacce shekara ne Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakar da al’umma a kan barnar da shaye-shayen miyagun kwayoyi ke yi ga rayuwar al’umma musamman matasa, barna ya munana, ta haka ake saran al’umma za su fahimci barnar da matsalar da ke tattare da nomawa da safarar muggan kwayoyi a cikin al’umma.
Abin takaici shi ne wannan gangamin na wannan shekarar yana zuwa ne a daidai lokacin da mu’amala da kwayoyi a tsakanin matasanmu take dada karuwa ne a kullum. Kidididgar da aka yi a shekarar 2019, ta nuna cewa, an fi shan tabar wiwi a tsakanin matasan inda aka gano cewa, akalla ‘yan Nijeriya fiye da Miliyan 10.6 ke shan tabar wiwi, inda wasu na fara shan tabar ne tun suna shekara 19 a duniya.
Haka kuma binciken wanda kungiyar ‘Global Drug Surbey’ ta gudanar ya nuna cewa, an fi shan kwayar ne a yankin Afrika ta Yamma.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa, tabar wiwi ce aka fi sha a yankin Afirka, inda aka samu kashi 5.2 zuwa 13.5 na masu shan tabar a yankin Afirka mafi yawansu kuma na yankin Afirka ta Yanma ne, ana kuma iya cewa, al’amarin kwayoyin ya yi kamari a Nijeriya fiye da wata kasa a Afirka.
Haka kuma a binciken da kungiyar ‘National Drug Use and Health Surbey’ ta gudanar a shekarar 2018, ta gano cewa, fiye da mutum 376,000 na cikin tsananin mu’amala da kwayoyi, inda daya daga cikin mutum 5 zaka samu daya yana amfani da kwayoyi da ake tsira wa da allura. Fiye da mutum 80,000 da ke amfani da allurar wajen zukar kwayoyin na fuskantar yada cututtuka kamar su Kanjamar da cutar hanta.
Babu kokwanto, nada Birgediya Janar Buba Marwa a mastayin shugaban Hukumar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi ya taimaka kwarai wajen zaburar da hukumar a yakin da ake yi da safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya.
Yana da muhimmanci a fahimci cewa a cikin wata 17 da suka wuce an samu nasarar kama masu safarar miyagun kwayoyi fiye da 17, 647 an kuma samu nasarar garkame manyan diloli masu safara kwayoyin 10, haka nan kuma hukumar ta samu nasarar zartar da hukunci a kan mutum 2,369 an kuma samu nasarar warkar da masu mu’amala da miyagun kwayoyin fiye 11,000 a daidai wanna lokacin da ake magana.
Ra’ayin wannan jaridar shi ne, ya zama dole a yi nasara a yakin da ake fuskanta a kan safara da amfani da miyagun kwayoyi saboda dangantakar miyagun kwayoyi da matsalar tsaro.
Idan za a iya tunawa a shekarar 2020, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya danganta yawaitar matsalar a kasar nan da yadda ake mu’amala da miyagun kwayoyi, ya kuma ce, lallai abin ya zama abin tayar da hankali.
A halin yanzu an dora Nijeriya a matsayin kasar da ta fi hatsari a kan ayyukan ‘yan ta’adda. A bin takaicin shi ne yadda harkokin ‘yan ta’adda ke kara karuwa a kullum suna cin karen su babu babbaka, duk da cewa, babu wani shashe na duniya da ya tsira daga abubuwan da suka shafi ayyukan ‘yan ta’adda amma lamarin Nijeriya yana da ban tsoro.
Don nuna jajircewarsa a kan yaki da miyagun kwayoyi, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a shekarar da ta gabata ya kaddamar da shiri na musamman da aka yi wa lakabi da ‘War Against Drug Abuse” (WADA)’ da kuma kundi na musanmman mai suna “National Drug Control Master Plan 2021-2025” na yadda za a fuskanci yaki da miyagun kwayoyi a sasan kasar nan.
Shugaban kasar ya kuma ce, barazanar da miyagun kwayo ke yi wa kasar nan ya fi na ayyukan ta’addanci da ake fuskanta.
Mun amince da bayanin shugaban kasa na cewa, miyagun kwayoyi ya taimaka wajen kara zafafa ayyukan masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda a sassan Nijeriya, mun kuma amince da irin nasarorin da NDLEA ke samu a yaki da miyagun kwayoyi, muna kuma kira da a kara kaimi wajen zafafa yakin da ake yi da masu safara da mu’amala da miyagun kwayoyi a sassan kasar nan ta haka za a tabbatar da rage lamarin yadda ya kamata.
Wannan yaki na kowa da kowa ne a saboda haka muna kira ga iyalai, makarantu da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran al’umma gaba daya su kawo nasu gudummawar don samun nasarar fatattakar masu safarar kwayoyi da masu mu’amala da ita, tare da kuma ba hukumar NDLEA goyon bayan da take bukata gaba daya.