Ƙungiyar ma’aikatan ruwa ta ƙasa (MWUN) ta bayyana aniyarta ta shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC da TUC suka kira a fadin ƙasar. Yajin aikin da za a fara a ranar Litinin 3 ga watan Yuni, martani ne ga gazawar gwamnatin tarayya na ƙara albashi mafi ƙaranci da kuma ƙin sauya farashin wutar lantarki da ta yi a baya-bayan nan.
Wannan mataki dai zai janyo rufe tashoshin jiragen ruwa a fadin ƙasar, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile ayyukan tattalin arziki a faɗin ƙasar baki ɗaya.
- NLC Na Gudanar Da Zanga-zanga A Ofishin KEDCO Na Kano Kan Ƙarin Ƙuɗin Wutar Lantarki
- Mafi Ƙarancin Albashi: NLC Za Ta Tsunduma Yajin Aiki
Shugaban ƙungiyar MWUN, Adewale Adeyanju, ya tabbatar da bin umarnin ƙungiyar NLC da TUC a wata sanarwa da shugaban yaɗa labaran ƙungiyar, Kennedy Ikemefuna ya fitar.
Adeyanju ya jaddada wajabcin yajin aikin ne saboda gazawar gwamnati kan muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziƙi da da ma’aikata. An umurci mambobin ƙungiyar a sassa daban-daban na ruwa da suka haɗa da tashar jiragen ruwa, jiragen sama, tashoshi, da tashoshin mai da iskar gas da su tabbatar da bin yajin aikin gaba ɗaya.
Wannan mataki dai na daga cikin dabarun da kungiyoyin kwadago ke yi na matsawa Gwamnatin Tarayya lamba wajen magance korafe-korafen ma’aikata, ciki har da kammala tattaunawa kan batun mafi karancin albashi na ƙasa da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarki.
Shigar da MWUN ta yi ya nuna rashin jin daɗi a tsakanin sassa daban-daban na ƙwadago da kuma yiwuwar kawo cikas ga harkokin tattalin arzikin Najeriya idan har matakin gwamnati bai canja ba.