Bayan ganawar sa’o’i huɗu da shugabannin majalisar dokoki da yammacin yau Lahadi a Abuja, ƙungiyar ƙwadago ta tabbatar da cewa za a gabatar gudanar da yajin aiki kamar yadda aka tsara a fadin ƙasar nan a ranar Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago (TUC) Festus Osifo ya bayyana cewa, matakin yajin aikin yana nan tsayin daka, kuma za su gabatar da koken Majalisar ga sassan ƙungiyarsu daban-daban, amma yajin aikin zai fara kamar yadda aka tsara.
- NLC Na Gudanar Da Zanga-zanga A Ofishin KEDCO Na Kano Kan Ƙarin Ƙuɗin Wutar Lantarki
- Mafi Ƙarancin Albashi: NLC Za Ta Tsunduma Yajin Aiki
Taron dai ya ƙunshi manyan mutane irin su shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, waɗanda suka yi yunƙurin hana ƙungiyoyin shiga yajin aikin saboda mummunan tasirin da zai iya yi ga al’umma da tattalin arziki Nijeriya.
Rikicin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ya samo asali ne daga taƙaddamar sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa da kuma ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan. Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun buƙaci a ƙara musu sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata, suna masu cewa ₦30,000 da ake biya a yanzu bai wadatar ba kuma ba dukkan gwamnoni ne ke biyan hakan ba.
Ƙungiyoyin dai sun tsayar da ranar 31 ga watan Mayu domin gwamnati ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi, amma tattaunawar ta ci tura, lamarin da ya kai ga ayyana yajin aikin.
Ƙungiyoyin sun yi watsi da tayin da gwamnati ta yi masu da dama, ciki har da na baya-bayan nan na ₦60,000, inda suke neman sabon mafi ƙarancin albashi na ₦497,000.
Haka suna son a duba cikar yarjejeniyar mafi ƙarancin albashin ma’aikata a halin yanzu, wanda ba a sake duba shi ba kamar yadda dokar ƙasa ta tanada na tsawon shekaru biyar a ƙarƙashin dokar mafi ƙarancin albashi na shekarar 2019.