Daga dukkan alamu hukumomin Saudiya sun samar da matakai na hana bakin haure da aka fi sani da Takari sakat a yayin gudanar da aikin hajjin bana na 2024.
Wakilinmu ya lura cewa, ‘yan Nijeriya maza da mata, wasu ma a kasar aka haifi iyayen su suna gudanar da harkokin saye da sayarwa na abinci da tufafi a kofofin Otal-otal da masallatan unguwannin da kuma hanyoyin zuwa masallacin Harami.
- Hajjin Bana: Saudiyya Ta Ba NAHCON Izinin Buɗe Asibitoci Biyu A Kasar
- Maniyyata Miliyan 1.2 Sun Iso Saudiyya Domin Hajjin Bana – Ma’aikatar Hajji Da Umrah
A wannan shekarar bayan katin shaida na NSUK da aka bukaci kowanne Alhaji ya makala a wuya a yayin zirga zirgarsa a garin Makka domin gane Alhajin gaskiya da na bogi, Askarawa suna sintiri a kai a kai suna fattakar bakin hauren, “Za ka ga sun rungumi buhunan kayan da suke sayarwa suna gudu, abin gwanin ban tausayi”, in ji Alhaji Bello Bala Bungudu.
Hukumar kasar Saudiyya ta haramta wa duk wanda ba shi da izinin gudanar da aikin hajji shiga garin Makka ko da kuwa dan kasar ne, inda ta ayyana hukuncin daurin shekara 6 ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin.
A tsokacinsa, wani dan jarida da ya dade yana shiga kasar Saudiya, Alhaji Kabir Yusuf, ya ce, yawancin irin wadannan mutanen suna shigowa ne da cikakken izini, ta hanyar zuwa Umara ko aikin Hajj ko kuma ta hannun kamfanonin daukar ma’aikata masu daukar ‘yan aikatau, amma da zaran takardar izinin zaman su ya kare sai su ci gaba da kulli kucciya tsakaninsu da jami’an tsaro.
Ya kara da cewa, a irin wannan ne zaka samu mutum ya yi shekaru a kasar, ya yi aure, ya hayayyafa, shida zuriyyarsa duk suna zama ba bisa ka’ida ba.
Ya ce, duk da halin matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a Nijeriya, ya kamata matasa su yi tunanin irin wulakancin da ake yi wa ‘yan Takari, “ Idan an kama mutum, bayan ya yi zaman gidan yari sai a kwace dukiyarsa a kuma fitar da shi zuwa wata kasar Afirka da karfin tsiya.
A kan haka ya shawarci gwamnati su farfado da tattalin azikin kasa ta yadda rayuwa zai yi dadi a Nijeriya.
Asibitocin NAHCON Sun Fara Aiki A Makkah
Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da samun amincewar Ma’aikatar Lafiya ta Kasar Saudiya ta bude cibiyoyin lafiya guda biyu a garin Makkah domin aikin kula da lafiyar Alhazai a garin Makkah.
Ma’aikatar Lafiya ta kasar Saudiyya ta mika sakon ne ta hannun Kungiyar Kwararrun Likitocinta da ke aikin kula lafiya a karkashin kamfanin Ithra Alkhair, a cikin wata takardar da ta aike wa ofishin Hukumar NAHCON da ke birnin na Makkah. Tuni kuma suka fara aiki gadangadan.
Bayanin da ke kunshe a cikin takardar ya nuna cewa manyan asibitocin guda biyu wadanda za a bude za su kasance ne a unguwannin da ke Masfala/Kudai da yankin Shari’e Al-Mansour, za kuma su ci gaba da aiki a matsayin manyan asibitoci, za kuma su yi jinyar manya da kananan matsalolin lafiya da ka iya tasowa daga Alhazai a zaman su na Makkah.
Dakta Abubakar Adamu Isma’eel, Shugaban bangaren Ma’aikatan Lafiya na NAHCON masu aiki a a cikin garin Makkah a wannan shekarar (2024) ne ya karbi takardar amincewar a madadin hukumar Alhazai na Nijeriya.
A jawabinsa Dakta Abubakar ya bayyana cewa, a halin yanzu suna da karin wasu asibitoci uku da suke jiran a basu amincewar gudanar da aiki nan gaba kadan, wanda haka zai samu damar bayar da cikakkiyar kulawa ga dukkan Alhazan Nijeriya.
Asibitocin guda uku da za a bude a nan gaba za su samu cikakkiyar amincewar yin aiki kamar yadda ya kamata.
A ana sa ran asibitocin za su yi aiki ne a masaukan Alhazai guda uku da suka hada masaukan Alhazan Nasarawa, Ogun, Oyo da kuma Masaukan Alhazan Jihar Borno.
Ya kuma kara da cewa za a samar da na’urar GPS na wuraren da Assibitocin suke nan da dan lokaci domin al’umma su samun saukin gane asibitocin.
Tuni dai Hukumar NAHCON ta tura tawagar kwararrun likitocin da ke shirin aiki tukuru domin kulawa da lafiyar Alhazan Nijeriya. Don haka Hukumar ta nemi hadin kan Alhazan Nijeriya domin samun nasarar wannan aiki.