Masu sharhi a kan wasanni a fadin duniya sun bayyana cewa abu ne mai wahala kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta je wasan karshe na wasan kofin Zakarunn Turai kuma a ce ta yi rashin nasara.
Borussia Dortmund ta fafata da Real Madrid a wasan karshe a Zakarunn Turai ranar Asabar a filin wasa na Wembley dake birnin London, kuma karo na 15 da suka fuskanci juna a tsakaninsu .
- Real Madrid Na Taimakawa Benzema Domin Murmurewa Daga Raunin Da Yake Fama Da Shi
- Champions League: Real Madrid Ta Zama Zakara Bayan Doke Dortmund
Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta bayar da mamaki da ta kawo matakin karshen a kakar wasa ta bana, bayan da ta ja ragamar rukuni na shida a Zakarunn Turai.
Kungiyar ce ta yi ta daya a rukunin da maki 11, sai Paris St Germain ta biyu da maki takwas da AC Milan ta uku da kuma kungiyar Newcastle United a gurbin da ya fi kowanne zafi.
Haka kuma kungiyar ta Jamus ta fitar da PSB a zagaye na biyu da yin waje da Atletico Madrid a wasan kusa da na kusa da na karshe doke kungiyar kwallon kafa ta PSG gida da waje a dab da karshe.
Ita ma kungiyar Real Madrid, ita ce ta ja ragamar rukuni na uku da maki 18, ta fuskanci kalubale da yawa, musamman a karawa da RB Leipzig da Manchester City da kuma Bayern Munich da ta kai wasan karshe. Real Madrid, wadda mai koyarwa Carlo Ancelotti ke jan ragama ta lashe gasar La Liga na bana kuma na 36 jimilla, hakan ya sa kungiyar ta yi iya yinta domin daukar Zakarunn Turai karo na 15 a tarihi.
Kungiyar Real Madrid, wadda ta kammala daukar Kylian Mbappe a wannan satin ta yi wasanni 12 ba tare da an doke ta ba a gasar Zakarun Turai ta kakar nan da yin nasara takwas da canjaras hudu. Ita kuwa Dortmund ta yi rashin nasara a wasa daya daga cikin wasanni 11 da ta fafata a gasar Zakarunn Turai da nasara bakwai da canjaras uku da yin wasa shida ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, kuma ita ce ke fara zura kwallo a raga karo tara daga fafatawa 10.
Wasan karshe a Zakarunn Turai da Dortmund ta buga shi ne a Wembley, inda ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Bayern Munich a shekarar 2013, kuma ‘yan wasanta Mats Hummels da Marco Reus sun taka rawar gani, wadanda har yanzu na buga wasa na tsawon shekara 11 a kungiyar. A hannu guda kuma Real Madrid ta sha fafatawa da kungiyoyin Jamus a wasan karshe, wadda sau daya ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Bundesliga daga 20 da cin 13 da canajaras shida a babbar gasar ta Zakarunn Turai.
Sau nawa kungiyoyin suka buga wasan karshe?
Wannan shi ne karo na uku da Dortmund ta kai wasan karshe a Zakarun Turai, yayin da Real Madrid ta yi karawa ta 18 a gasar da lashe 14 daga ciki sannan Dortmund ta yi nasarar doke Jubentus a wasan karshe a 1997 da rashin nasara a hannun Bayern Munich a fafatawar karshen a 2013.
Ita kuwa Real Madrid ta yi rashin nasara uku a wasan karshe, kuma na baya-bayan nan shi ne a 1981, sannan wannan shi ne karo na 15 da za su fafata a tsakaninsu kuma duka a Zakarunn Turai, inda Dortmund ta yi nasara uku da canjaras biyar, Real Madrid ta ci wasa shida.
Real Madrid ce kan gaba a yawan lashe Zakarun Turai a tarihi, mai 14 jimilla, yayin da Dortmund take da daya a tarihi, sannan rabon da Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Jamus tun 2013 a hannun Borussia Dortmund.
Bugu da kari wannan shi ne wasan karshe karo na biyar tsakanin kungiyar Jamus da ta Sifaniya a ko dai European Cup ko kuma kofin Zakarun Turai, sannan kowacce ta yi nasara bibiyu, inda Bayern Munich ta doke Atletico Madrid a 1974 da kuma cin Balencia a 2000. Ita kuwa Real Madrid ta yi nasara a kan Eintracht Frankfurt a 1960 da doke Bayern Leberkusen a 2002.
Da a ce Dortmund ta lashe wasan karshe a Wembley ranar Asabar din da ta gabata da tuni ta zama kungiya ta hudu da ta dauki kofin da tazara mai yawa tsakani da kofin farko, wato daga 1997 zuwa 2024, kenan shekara 27 tsakani.
Wacce take da tazarar daukar kofi da yawa ita ce Inter Milan, shekara 45 da ta lashe kofin farko 1965 na Zakarun Turai, sai ta dauki na gaba a shekarar 2010 a lokacin Jose Mourinho.
Dortmund ta ci kungiyar Sifaniya, Atletico Madrid a zagayen dab da na kusa da na karshe a bana, hakan yana nufin ta doke kungiyar daga kasar Sipaniya 7-3 a irin wannan gurbin.
Dortmund ta yi nasara a kan AJ Auderre a 1993 da kuma Rangers a 1999, amma ta yi rashin nasara a hannun Club Bruges a 2003 da kuma Udinese a 2008 a Zakarun Turai duka a bugun daga kai sai mai tsaron raga. Wasan da Dortmund ta fafata a filin wasa na Wembley ranar Asabar shi ne na 300 a gasar Zakarunn Turai, kuma kungiyar sai da ta yi shekara 41 sannan ta yi fafatawa ta 100 daga 1956 zuwa 1997.
Haka kuma Dortmund ta yi shekara 17 sannan ta kara yin wasa na 100, kuma na 200 jimilla tsakanin 1997 zuwa 2014).
Sai kuma ta yi shekara 10 da ta kara wasa na 100 kuma na 300 a gasar Zakarun Turai tsakanin 2014 zuwa 2024 haka kuma a wasanta na 100 a gasar Zakarun Turai, Borussia ta doke Jubentus 3-1 ta kuma lashe kofin. A bangaren Real Madrid kuwa Borussia Dortmund ita ce kungiya ta hudu da Real Madrid za ta fafata da wadda ke buga Bundesliga a Zakarun Turai a kakar wasa ta bana.
Real Madrid din ta doke Union Berlin 1-0 a gida da kuma 3-2 a waje a cikin rukuni na uku sannan kuma ta doke Leipzig 1-0 a Jamus, sannan suka tashi 1-1 a Sifaniya bayan an fito daga rukuni.
Sai kuma kungiyar ta Real Madrid ta fuskanci Bayern Munich, wadanda suka tashi 2-2 a Jamus, sannan ta yi nasara 2-1 a filin wasa na Santiago Bernabeu a zagayen dab da karshe. A shekara ta 2017, Real Madrid ta zama ta farko da ta kare kofinta na Zakarun Turai, sannan ta zama ta farko da ta lashe uku a jere a 2016 da 2017 da kuma 2018.
Wannan shi ne wasan karshe na 22 da Real Madrid ta fafata a dukkan gasar Zakarunn Turai.
Kuma a kofi 17 da take da shi a European Cup/Zakarun Turai ta dauki UEFA Cup a 1985 da kuma 1986, sai ta yi rashin nasara a wasan karshe a European Cup Winners’ Cup a 1971 da kuma 1983.
A wasan da Real Madrid ta buga da kungiyoyin Jamus tun daga zagaye na biyu ta yi nasara 20 da kai wa zagayen gaba karo takwas.
Sau nawa Real Madrid da Borussia Dortmund suka hadu?
Kungiyoyin Real Madrid da Borussia Dortmund sun hadu a gasar Zakarun Turai sau 14 a tsakaninsu, inda Real Madrid ta ci wasa shida da canjaras biyar, Dortmund ta ci wasanni uku. Kuma sun hadu ne a gasar Zakarun Turai, inda suka fara fuskantar juna
ranar 1 ga watan Afirilun 1998, inda Real Madrid ta yi nasarar cin 2-0, sai wasa na biyu kuwa da aka yi a Jamus ranar 15 ga watan Afirilu, sun tashi ba ci a fafatawar.
To sai dai wannan shi ne karon farko da suka fafata a wasan karshe a babbar gasar ta Zakarunn Turai. Jerin wasannin da aka yi tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund:
2017/2018
Zakarun Turai Laraba 06 ga watan Disambar 2017 Real Madrid 3 – 2 B Dortmund
Zakarun Turai Talata 26 ga watan Satumbar 2017-B Dortmund 1 – 3 Real Madrid
2016/2017.
Zakarun Turai Laraba 07 ga watan Disambar 2016. Real Madrid 2 – 2 B Dortmund
Zakarun Turai Talata 27 ga watan Satumbar 2016 B Dortmund 2 – 2 Real Madrid
2013/2014-
Zakarun Turai Talata 08 ga watan Afirilun 2014- B Dortmund 2 – 0 Real Madrid
Zakarun Turai Laraba 02 ga watan Afirilun 2014. Real Madrid 3 – 0 B Dortmund
2012/2013
Zakarun Turai Talata 30 Afirilun 2013. Real Madrid 2 – 0 B Dortmund
Zakarun Turai Laraba 24 ga watan Afirilun 2013- B Dortmund 4 – 1 Real Madrid
Zakarun Turai Talata 06 ga watan Nuwambar 2012- Real Madrid 2 – 2 B Dortmund
Zakarun Turai Laraba 24 ga watan Oktoban 2012- B Dortmund 2 – 1 Real Madrid
2002/2003
Zakarun Turai Talata 25 ga watan Fabrairun 2003- B Dortmund 1 – 1 Real Madrid
Zakarun Turai Laraba 19 ga watan abrairun 2003- Real Madrid 2 – 1 B Dortmund
1997/1998
Zakarun Turai Laraba 15 ga watan Afirilun 1998- B Dortmund 0 – 0 Real Madrid
Zakarun Turai Laraba 01 ga watan Afirilun 1998-Real Madrid 2 – 0 B Dortmund