• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyara A TETFund: Gwamnan Zamfara Ya Nemi Ƙarin Tallafi Ga Manyan Makarantun Jihar

by Leadership Hausa
1 year ago
zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci ƙarin tallafi daga Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na TETFund, domin kammala wasu gine-ginen a manyan makarantun Jihar.

Gwamnan ya yi wannan roƙo ne a wata ziyarar aiki da ya kai hedikwatar Hukumar ta TETFUND a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamnan ya buƙaci tallafi, musamman ga Jami’ar Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau.

Ya ƙara da cewa, Jami’ar jihar da ke Ƙaramar Hukumar Talatan Mafara tana da ayyuka da dama waɗanda gwamnatocin baya suka fara kuma suka yi watsi da su.

“Lokacin da na ziyarci TETFund, na ambaci cewa a kullum neman ƙari muke yi. A yau, na zo ne don neman ƙarin tallafi ga wasu manyan makarantun Zamfara.

LABARAI MASU NASABA

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

“Na ziyarci Karamar Hukumar Talata Mafara makonni biyu da suka wuce na ga ayyukan da TETFUnd ta gudanar a Jami’ar Jihar Zamfara. Abin takaici, akwai ayyuka da yawa da aka yi watsi da su a zamanin gwamnatocin baya.

zamfara

“Muna fuskantar matsaloli game da gyaran Kwalejin Fasaha ta Abdu Gusau, kuma ina buƙatar goyon bayanku don warware wannan matsala.

“Zamfara na fama da ƙalubale daban-daban baya ga matsalar rashin tsaro. Lokacin da muka karɓi mulki a shekarar da ta gabata, ba a biya ma’aikata albashi ba na tsawon watanni uku, kuma ɗalibanmu ba su iya biyan kuɗin jarrabawar WAEC da NECO. Har ila yau, muna da ɗalibai da yawa a kan tallafin karatu a ƙasashen Cyprus, Indiya, da Sudan waɗanda ba a kula da su ba, da sauran batutuwan gaggawa.

“Gwamnatina ta warware matsalar albashin ma’aikata, ta biya bashin da ake bi na WAEC da NECO, sannan ta sasanta tare da daidaita biyan ɗaliban da za su samu tallafin karatu a ƙasashen waje. Mun zo nan ne domin neman taimakon ku, wanda zai taimaka sosai a ƙoƙarinmu na ceto da sake gina Zamfara.”

Da yake mayar da martani, Sakataren Zartarwa na Asusun, Arc Sonny T. Echono ya yaba wa Gwamna Lawal bisa nasarorin da ya samu a shekarar farko da ya yi kan mulki.

“Ina so in taya ka murnar cika shekara guda a kan karagar mulki, kuma ina so in yaba maka kan ayyukan da ka ke yi a ma’aikatun gwamnati, cibiyoyi, asibitoci, da sauran fannoni.

  • Tsoho Mai Shekara 70 Ya Shiga Hannu Kan Safarar Wiwi

 

“Za mu sake duba buƙatar gwamna, kuma mu yi duk mai yiwuwa. Yunƙurin da ka ke yi wajen magance al’amuran jihar abin yaba wa ne kuma ya nuna babban matsayi, ni kaina ina so in gode maka kan daidaita bashin WAEC da NECO,” in ji Echono.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba
Ilimi

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi
Ilimi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Minista Nnaji Ya Yi Ƙarar Jami’ar UNN Kan Rikicin Takardun Kammala Makaranta
Ilimi

Minista Nnaji Ya Yi Ƙarar Jami’ar UNN Kan Rikicin Takardun Kammala Makaranta

October 6, 2025
Next Post
Sinadarin Ƙara Kuzari Lokacin Jima’i

Sinadarin Ƙara Kuzari Lokacin Jima'i

LABARAI MASU NASABA

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

October 18, 2025
Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Radda

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

October 18, 2025
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

October 18, 2025
IMF

Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF

October 18, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.