An dakatar da wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Rangers da Enyimba a yau Lahadi sakamakon cika filin wasa da magoya bayan kungiyoyin biyu suka yi a wasan mako na 35 na gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL).
Wasan da aka yi wa lakabi da Oriental Derby ya gamu da cikas a lokacin da magoya bayan Enyimba suka ki amincewa da matakin da alkalin wasa ya yanke na ba wa Rangers bugun fanareti yayin da wasan ya dau zafi, Rangers ke saman teburin gasar (maki 60) sai Enyimba take biye mata da maki biyu a tsakaninsu.
- Yaushe Za A Fara Kofin Duniya Na Kungiyoyi?
- An Buga Jadawalin Zagaye Na 16 Na Gasar Europa Da UEFA Conference League
Magoya bayanta sun yi dafifi inda suka hana alkalin wasan ya ida nufinsa, hakan ya janyo yan wasan Enyimba ficewa daga cikin filin wasan, wannan hukuncin bai yi wa yan wasan Enyimba dadi ba wadanda suka nuna rashin amincewarsu da matakin.