Duba da yadda abubuwa suka sake tabarbarewa, musamman idan aka yi la’akari da bangaren da ya shafi tattalin arzikin wannan, abin ba a cewa komai; domin kuwa mafi yawan magi-danta sun samu kansu a wani hali irin na ha’ula’i.
A daidai wannan lokaci, rayuwa ta zama abin da ta zama;domin kuwa komai ya yi matukar tsada, mafi yawan abubuwan da aka sani daga shekara uku zuwa yanzu; kudinsa ya ninka kusan sau uku ko hudu ko ma sau biyar, duk da cewa masu daukar albashi ba wai karuwa albashin nasu ya yi ba.
- Babbar Sallah: Tsadar Tumatir Na Barazana Ga Armashin Bikin
- Gwamnantin Zamfara Ta Fara Biyan Albashin Watan Yuni Domin Hidimar Sallah
Wannan yanayi da aka tsinci kai a ciki, wajibi ne ya tilasta wa maigida neman hanyar da za ta taimaka musu wajen samun sas-sauci a cikin wannan rayuwa. Don haka, ya zama lallai magid-anci ya sauya taku; ta hanyar rage wa kansa wasu hidindimu na babu gaira babu dalili. Sannan, ko da miyar da ake yi masa a gida a da sai da nama, ya kamata ya san cewa yanzu lokacin ya canza.
A bangare guda, ita ma uwargida na da tata gudunmawar da za ta bayar a rayuwrsu ta yau da kullum. Saboda haka, uwargida akwai yadda za ki hada miyarki ta yi dadi ba tare da kin sa mata nama ba, domin kuwa abin da miya ta fi bukata ita ce albasa, za ki iya yin miyarki babu nama; amma kuma ki sa mata albasa sosai, miyar taki za ta yi dadi kamar kin yi ta da nama, don ba ki sa nama a miya ba; ba shi ne zai hana miyarki yin dadi ba, rashin albasa kawai ita ce matsala.
Duk da cewa, mun shigo wani yanayi na tsadar kayan miya, musamman ma tumatur, ya yi matukar tsada ga shi kuma dole ana bukatarsa da dan yawa; wasu ma na sa shi ya fi tattasai ya-wa, saboda ya kashe zafin yaji. Don haka, a nan uwargida za ki iya sayen tattasai ya fi tumatirin yawa, idan kuma shi ma tat-tasan tsadarsa ta yi yawa; za ki iya hadawa da shambu ko kuma ma shambun zalla za kuga miyar ta yi armashi ga wadanda ba sa cin yaji. Sannan, idan kin tashi gyara shambun din ko tat-tasai; sai ki cire ‘ya’yansa da ke ciki da kuma dan jijiyar, saboda su ne suka fi yaji.
Har ila yau, akwai kuma wani salon da uwargida za ki bi wajen yin miyarki; ba tare da kin sa mata tumatur ba, za ta yi dadi kamar yadda na fada miki a baya; albasa ce dadin miyar za ku-ma ki iya amfani da tattasai ko shambun ki dan sa su da dan yawa, sai albasa ita ma ki sa ta da yawa sosai; za ki ga miyar taki ta yi kyau ta kuma yi dadi ba tare da kin sa tumatur ba.
Haka zalika, akwai kalolin abinci da dama; wadanda ba sai kin yi amfani da kayan miya ba, kamar shinkafa da wake, taliyarki idan kika samu siri-siri kika dafa ta fara, kika soya manjanki ya ji albasa; sannan sai ki kawo magi da yaji ki sa kowa da kowa a gida ya ci.
Haka nan, ita ma shinkafa ta yi matukar tsada, idan ba a samu shinkafa ba; ba dole ne sai an ci ta ba, akwai tuwon masara yana da dadi sosai; saboda haka sai ki gyara masararki a bayar a nika, domin ita amfani biyu ma ko uku za ki iya yi da ita; ko dai tuwon laushi ko burabusko ko kuma danbunta.
Kazalika, idan masarar ita ma ba ta samu ba; akwai dawa ita ma ana yin tuwo da ita, sannan kuma ga alkama ita ma amfani biyu za ki iya yi da ita; akwai tuwon laushi da kuma na buski.
Bugu da kari, sakamakon karatowar Babbar Sallah, ya kamata maigida ya sani cewa; layya ba wajibi ba ce ga wanda ba shi da hali ko iko, ballantana ya matsa wa kansa sai ya yi, illa kawai dai saboda yara za ku iya soya ‘yan kajinku; shi ma idan akwai hali, idan babu kuma sai a hakura.
Saboda haka, ya kamata uwargida ta taimaka wa maigidanta tare da kuma tausaya masa duba da wannan hali da ake ciki yanzu, har batun abincin Sallah, idan babu hali ba dole ne sai kin kashe kudi mai yawa ba, duk abin day a samu sai a yi hakuri a karba a haka; wata rana sai labari.