Kusan shekara guda daya da kaddamar da majalisa ta 10, amma har yanzu akwi sanatoci 24 ciki 109 daga sassan kasar nan da ba su kawo ko da kudiri guda daya ba a zauren majalisar dattawa. Sauran sanatocin guda 85 sun gabatar da kuduri daya ko fiye da haka.
An dai kaddamar da zauren majalisar dattawan ne a ranar 13 ga Yunin 2023, yayin da a yanzu ta zarce shekara guda. Bincike ya nuna cewa a zuwa yanzu an gabatar da kudirori 279 a zauren majalisa a tsakanin ranar 13 Yulin 2023 zuwa Maris ta 2024.
Daya daga cikin muhimman ayyukan ‘yan majalisa shi ne, su gabatar da kudirin kan abubuwan da suke ci wa al’ummarsu tuwo a kwarya a zauren majalisa.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Majalisa Za Ta Karbi Ƙudurin Sabon Mafi Karancin Albashi – Tinubu
- ‘Yan Majalisar Wakilai Sun BuÆ™aci A Mayar Da Wa’adin Mulkin Nijeriya Falle ÆŠaya Mai Shekaru 6
Majalisar dattijai tana da mambobi 109, wanda 14 daga cikinsu tsofaffin gwamnoni ne, sai biyu daga cikin sanata da suka hada da Dabid Umahi (APC, Ebonyi ta Kudu), da Ibrahim Geidam (APC, Yobe ta Gabas) ne Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada ministocin ayyuka, da harkokin ‘yansanda.
Adadin tsoffin gwamnoni a majalisar dattawa ya karu bayan zuwan tsohon gwamnan Jihar Filato, Sanata Simon Lalong (APC, Filato ta Kudu) wanda aka rantsar da shi a matsayin sanata a watan Disambar 2023, don maye gurbin Sanata Napoleon Bali (PDP, Filato ta Kudu) bayan hukuncin kotun daukaka kara.
Idan za a iya tunawa an rantsar da Sanata Ani, Dachungyang da Mustapha cikin majalisar dattawan a makare bayan da ‘yan majalisar suka tafi hutu. Yayin da Ani ya maye gurbin Umahi, Dachungyang ya maye gurbin tsohon shugaban marasa rinjaye, Mwadkwon Simon Dabou, sannan Mustapha ya maye gurbin Ibrahim Geidam.
Tsoffin gwamnonin da yanzu haka suke majalisar dattawa ta 10 su ne guda 13 da suka hada da Orji Uzor Kalu (APC, Abiya ta Arewa); Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio (APC, Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma); Seriake Dickson (PDP, Bayelsa ta Yamma), Adams Oshiomhole (APC, Edo ta Arewa), Ibrahim Dankwambo (PDP, Gombe ta Arewa), Danjuma Goje (APC, Gombe ta tsakiya), Adamu Aliero (PDP, Kebbi ta tsakiya), Sani Bello (APC, Neja ta Arewa), Gbenga Daniel (APC, Ogun ta Gabas), Aminu Tambuwal (PDP, Sakkwato ta Kudu), Aliyu Wammako (APC, Sakkwato ta Arewa), Simon Lalong (APC, Filato ta Kudu da Abdulaziz Yari (APC, Zamfara ta Yamma).
Daga cikin tsofaffin gwamnoni 13, tara ne suka gabatar da kudirin a cikin wa’adin da aka yi nazari akai, wanda suka hada da Orji Uzor Kalu, kudiri 5; Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, biyu; Sanata Gbenga Daniel, 4; Sanata Dankwambo, 3; Aminu Tambuwal, 1; Sani Bello, 3; Danjuma Goje, 2; Wammako, 5; da Adamu Aliero, 1.
Cikin tsoffin gwamnonin da har yanzu ba su gabatar da wani kudirin doka ba a tsawon wannan lokaci sun hada da Sanata Adams Oshiomhole da Henry Seriake Dickson da Simon Lalong da kuma Abdulaziz Yari.
Sanatoci 24 baya ga tsofaffin gwamnoni hudu da har yanzu ba su dauki nauyin kowani kudiri ba sun hada da Sanata Ahmad Lawan (APC, Yobe ta Arewa), Bictor Umeh (LP, Anambra ta tsakiya), Oluwole Fasuyi Cyril (APC, Ekiti ta Arewa), Titus Tartenger Zam ( APC, Benuwai ta Arewa maso Yamma), Peter Jiya (PDP, Neja ta Kudu), Adegbonmire Adeniyi Ayodele (APC, Ondo ta tsakiya), Oyewumi Kamorudeen Olalere (PDP, Osun ta Yamma), Anthony Ani (APC, Ebonyi ta Kudu), Imasuen Neda Bernards ( LP, Edo ta Kudu); Okechukwu Ezea (LP, Inugu ta Arewa), Chukwu Chizoba (LP, Inugu ta Gabas), Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta tsakiya), Khabeeb Mustapha (PDP, Jigawa ta Kudu maso Yamma) da Kaila Samaila Dahuwa (PDP, Bauchi ta Arewa).
Sauran sun hada da Sanata Rufai Hanga (NNPP, Kano ta tsakiya), Abdulaziz Yar’Adua (APC, Katsina ta tsakiya), Mohammed Dandutse Muntari (APC, Katsina ta Kudu), Enyinnaya Abaribe (APGA, Abiya ta Kudu), Pam Dachungyang (ADP, Filato ta Arewa); Onyesoh Allwell Heacho, (PDP, Ribas ta gabas); Ibrahim Lamido (APC, Sakkwato ta gabas), Manu Haruna (PDP, Taraba ta tsakiya) da Musa Mustapha (APC, Yobe
ta gabbas).