A yayin da aka kammala jigilar alhazan bana a ranar Lahadi 10 ga watan Yuni 2024 ba tare da wata matsalar a zo a gani ba, Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON ta ayyana ranar 22 ga watan Yuni na fara dawo da Alhazai gida bayan kammala aikin hajjin.
Domin tabbatar da an gudanar da aikin hajjin cikin nasara, Hukumar Alhaza NAHCON tare da Ma’aikatar Aikin Haji da Umara ta kasar Saudiya sun jagoranci shugabannin hukumar Alhazai na jihohi, ‘yan jarida da wakilan masu ruwa da tsaki zagayen gani da ido domin ganin irin shirin da hukumar ta yi a wurare masu tsarki da za su karbi bakuncin miliyoyin Alhazai daga sassan duniya, wuraren sun hada da Muna, Muzdalifa da kuma Arafat.
- Hajjin Bana: Ofishin Jakadancin Saudiyya Ya Yi Bankwana Da Alhazan Nijeriya
- Sabon Tsari: Alhazan Nijeriya Zasu Daina Daɗewa A Saudiyya
Jihohin da suka samu halartar wannan zagayen sun hada da Jihar Nasarawa, Oyo, Ogun, Kaduna, Kano, Yobe da kuma jihar Filato, sauran jihohin sun kuma hada da jihar Benuwai, Kebbi, Katsina, Sakkwato Zamfara da Jigawa. Haka kuma an samu hakartar ‘yan jarida daga kafafen watsa labarai da dama na gida Nijeriya da dana kasashen waje.
Shugaba mai kula da harkokin NAHCON a garin Makkah, Dakta Aliyu Tanko da Kwamishina mai kula da gudanarwa na NAHCON Prince Anofiu Olarenwaju Elegushi suka jagoranci zagayen, inda Dakta Aliyu Tanko ya bayyana irin shirin da hukumar kasar Saudiya ta yi a bangaren sake fasalin tantin da Alhazai za su zauna a ciki, inda aka sabunta na’urorin sanyaya dakuna (AC) a dukkan tantunan an kuma samar ban dakuna a kusa-kusa domin walwala da jin dadin Alhazai.
Wakilinmu ya kuma lura da yadda aka tanadi jami’an tsaro a dukkan bangarorin na Muna, Muzdalifa da kuma Arafat, “An samar da jami’an tsaron ne don tabbatar da komai ya tafi daidai a kuma samu nasarar dakile duk wata barazana da ka iya tasowa a yayin gudanar da wannan ibadar, ba ma son irin abin da ya faru a shekarun baya na turmutsitsi ya sake faruwa, inda ya yi sanadiyyar rasuwar Alhazai ‘yan Nijeriya 300,” in ji Dakta Aliyu Tanko.
A kan haka, Dakta Aliyu Tanko ya nemi hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki, musamman shugabannin alhazai na jihohi da ‘yan Jarida su karfafa gangamin fadakar da alhazai a kan bukatar bin doka da oda, su kuma bi umarni da dokokin da aka tsara a wadannan wuarre masu tsarki domin ganin an samar nasarar da ya kamata.
A nasa tsokacin, kwamishinan NAHCON mai kula da ayyuka Prince Anofiu Olarenwaju Elegushi, ya ce makasudin wannan ziyarar, ita ce domin hukumoimin Alhazai na jihohi sun fahimci irin tsarin da aka yi a wannan shekarar domin su san yadda za su ilimantar da alhazan su ta yadda za a kauce wa rudani a yayin gudanar da aikin hajji, “Zagayen wadannan wuraren ibada zai taimaka wa jami’an hukumar Alhazai sanin yadda za su tafiyar da alhazansu a wurare masu tsarki na Muna, Arafat da kuma Muzdalifa.
Ya kuma nemi Alhazai su kare kansu daga tsananin zafin da za a fuskanta a ‘yan kwanakin nan a kasar Saudiya, saboda haka su guji yawo a cikin rana ba tare da wani dalili ba, “Dokokin addnin Musulunci ba su ce dole sai mutum ya hau kan dutsen Arafat (Jabalur-Rahma) ba a yayin tsayiwar Arfat, wannan ma ya zama dole saboda irin cutar da za a iya fuskanta a wannan lokacin,’’ in ji shi.
A wani bangaren kuma Hukumnar Alhazai ta NAHCON ta sanar da samun nasarar jigilar Alhazan bana daga jihohi 15, sun kuma hada da Kaduna, Bauchi, Bayelsa, Benuwai, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Oyo, Osun, Taraba, Ribas da kuma alhazai na bangaren runudunoni tsaro.
Sauran jihohin da aka kammala jigilar Alhazan jihohisu sun hada da Kebbi, Adamawa, Borno, Gombe, Jigawa, Kwara, Ogun, Yobe da yankin Babban Birni Tarayya Abuja, inda Alhazan wadannan jihohin da dama suka gama zaman su na garin Madina kuma sun isa garin Makka domin gudanar da ainihin aikin hajjin bana.
Idan ba a manta ba kamfanonin jirage uku ne suka yi jiglar Maniyyatan Nijeriya zuwa kasa mai tsarki a wannan shekarar sun kuma hada da Flynas, Mad Air da kuma Air Peace.
Ya zuwa ranar Asabar din nan kamfanin jigilar Alhazai na Flynas ya yi sawu 45 da adadin Maniyata 18,727 abin da ya bashi kashi 94% cikin dari na jigilar Maniyatan da zai kwasa daga gida Nijeriya zuwa kasa mai tsarki.
Kamfanin Mad Air ya yi sawu 48 inda ya dauki adadin Maniyata 23,233 abinda ya bashi kashi 97% cikin dari na Maniyatan da yake jigila.
Haka kuma kamfanin jiragen sama na Air Peace ya yi sawu 24 ya yi jigilar Alhazai 7, 293.
Bayanin da ya fito daga shasin tattara bayanai na NAHCON, kamfanonin jiragen saman gaba dayan su sun yi sawu 117 nda a ciki suka kwashi alhazai fiye da 49,253.
Daga cikin wannan adadin Maniyyata 7,566 ne kadai suka sauka a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jidda, jirage 101 duk sun sauka ne a filin saukar jirage na Yarima Muhammad bin Abdulaziz da ke Birnin Madinah.
A yawan Maniyyata 49,253 da muke da su a Kasar ta Saudiya, Maniyyata maza muna da mutum 30,658 yayin da muke da maniyyata mata 18,595.
Daga cikin adadin jimlar, Maniyata 10,525 ne suke birnin Madina, inda Maniyata 38,728 suka kammala aikin Umura, suna zaune a garin Makkah suna jiran lokacin fita Muna domin gudanar da aikin Hajji na wannan shekara 2024.