Najeriya ta koma matsayi na 38 a sabon jadawalin hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA), abin da ya yi matukar raguwa daga matsayi na 30 da take a baya.
A yanzu Super Eagles tana da maki 1498.93, inda ta ragu da maki 1520.27, wanda hakan ke nuna gazawar da ta yi a baya-bayan nan.
Tawagar ta yi kunnen doki 1-1 da Afrika ta Kudu, sannan ta sha kashi a hannun jamhuriyar Benin da ci 2-1, wanda hakan ya taimaka wajen faÉ—uwar ta a matsayi.
FaÉ—uwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen tunkarar wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026, abin da ke jefa shakku kan makomar Najeriya.
A halin da ake ciki, Argentina ta ci gaba da zama ta daya da maki 1860.14, yayin da Faransa da Belgium suka kasance na biyu da na uku. Brazil ta koma matsayi na hudu, inda ta wuce Ingila, wadda ta koma ta biyar.
Sauran sun haɗa da ƙasar Laberiya ta haura matsayi 10 zuwa na 142 sai Equatorial Guinea ta faɗo matsayi 10. Morocco ta ci gaba da zama a matsayi mafi girma a Afirka a matsayi na 12, sai Senegal a matsayi na 18.
An shirya sabunta jadawalin FIFA na gaba a ranar 18 ga Yuli, bayan kammala UEFA EURO 2024 a Jamus.