Adadin waɗanda suka mutu a aikin Hajjin bana a Saudiyya ya kai 1,301 a hukumance, inda aka bayyana matsanancin zafi da kuma shiga ƙasar ba tare da izini a matsayin manyan dalilai.
Gwamnati ta ba da rahoton cewa kashi 83% na waɗanda suka mutu mahajjata ne ba tare da izini ba waɗanda suka yi doguwar tafiya a ƙarƙashin rana mai zafi ba tare da matsugunin da suka dace ba, lamarin da ya haifar da matsalolin zafi da yawa.
Yanayin zafi a Makka ya haura sama da ma’aunin 125, abin da ya sa mahajjata da dama suka durƙushe saboda gajiyar tafiya da kuma zafi.
- Saudiyya Ta Gargaɗi Maniyyata Kan Tsananin Zafi
- Hajji 2024: Sarki Salman Na Saudiyya Ya Bai Wa Mahajjata Kyautar Al-ƙur’ani Mai Girma
Yawaitar mahajjatan da ba a ba su izinin aikin Hajji ba, sakamakon zuwa a hukumance yana da tsada, wanda hakan ya sa wasu alhazai suka bi ta hanyoyi masu haɗari don zuwa Saudiyya.
A baya-bayan nan ne mahukuntan Masar suka soke lasisin wasu kamfanonin yawon buɗe ido 16 saboda gudanar da tafiye-tafiye ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da aka ce ya tilasta wa ɗaruruwan ƴan ƙasar ta Masar shiga cikin munanan hanyoyin hamada ba tare da takardar izinin shiga kasar ba, lamarin da ya sa suka fuskanci tsananin zafi.