Wata babbar kotun jihar Kano ta ɗage sauraren ƙarar da gwamnatin jihar Kano ta shigar a kan Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da wasu sarakuna huɗu zuwa ranar 2 ga Yuli, 2024. Shari’ar na neman hana su gabatar da kansu a matsayin Sarakuna.
Mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta saurari kowanne ɓangare biyun, ciki har da lauyan Aminu Ado, Barr. Ibrahim Muktar, da kuma na gwamnatin jihar Kano, Barr. Ibrahim Isah-Wangida.
- Manoman Kano Da Kaduna Za Su Amfana Da Shirin Yaki Da Cutar Tumatir
- Rikicin Masarautar Kano: An Tura Ƙarin ‘Yansanda Fadar Ƙofar Kudu Da Gidan Nassarawa
Kotun dai ta shirya yin hukunci ne kan wata buƙata gami da umarnin shiga tsakani biyo bayan umarnin wucin gadi da aka bayar a baya.
Sai dai lauyoyin Aminu Ado sun shigar da wata sabuwar buƙatar a gaban kotu, inda suka bukaci ƙarin shigar da wasu cikin waɗanda ya kamata su bayar da jawabi. Sun haɗa da; ragowar sarakuna da hukumomin tsaro.
A baya dai, yunƙurin kai wa waɗanda ake ƙara takardar gayyata ya samu cikas, bayan da wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin hana cin zarafi da tsoratarwa, kamar yadda Abdulsalam Saleh, lauyan Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP) ta bayyana.
Mai shari’a Amina Adamu ta ba da umarnin a bi ta hannun kwamishinan Ƴansandan jihar Kano wajen isar da ita gayyatar, tare da sanya ranar 24 ga watan Yunin 2024 a matsayin ranar ci gaba da sauraron ƙarar.
A yayin ci gaba da shari’ar, lauyan Aminu Ado ya buƙaci a yi watsi da ƙarar, yana mai bayar da hujjar rashin hurumin kotun. Amma lauyan gwamnati ya tabbatar da hurumin kotun kuma ya buƙaci a ci gaba da sauraren karar.
Mai shari’a Amina Adamu ta ɗage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Yuli, 2024, domin ci gaba da tattaunawa kan waɗannan batutuwa da kuma ci gaba da shari’a. ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 2 ga watan Yuli, 2024, domin ci gaba da tattaunawa kan waɗannan batutuwa da kuma ci gaba da shari’a.