Uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da uwargidan shugaban kasar Poland Agata Kornhauser Duda, sun ziyarci cibiyar gabatar da wasannin fasahohi (NCPA) dake birnin Beijing.
A cewar Peng Liyuan, Sin da Poland na da daddaden tarihi da al’adun gargajiya masu zurfi, kuma musayar al’adu da mu’amalar jama’a tsakaninsu na kara kyautatuwa a shekarun baya bayan nan. Ta kara da cewa, da ingantuwar musayar al’adu, fahimtar juna da abota tsakanin al’ummomin kasashen biyu za su kara zurfi.
A nata bangare, Agata Kornhauser Duda wadda ta rako mijinta a ziyarar aiki da yake a kasar Sin, ta ce tana sa ran ganin karin musaya da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da ingantuwar abota tsakanin jama’arsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)