Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana a yau a yayin taron tattaunawa na wakilan masana’antu da cinikayya na kasa da kasa na dandalin tattaunawa na Davos na lokacin zafin na shekarar 2024 cewa, kasar Sin za ta samar da karin dama da yanayi mai kyau ga masu zuba jari na kasa da kasa. Sin tana maraba da masu zuba jari su ci gaba da zuba jari da aiwatar da ayyuka a kasar Sin, da cin gajiyar bunkasuwar kasar Sin mai inganci.
Ban da wannan kuma, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin ta fitar da motoci masu amfani da wutar lantarki zuwa kasashen waje don biyan bukatun kasuwannin kasa da kasa. Kayayyakin Sin suna da inganci, an samar da su ba tare da samun rangwame ba. Kasar Sin ba ta sabawa ka’idojin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO da suka shafi rangwame ba.
- Xi: A Shirya Sin Take Ta Daukaka Dangantakarta Da Poland Zuwa Sabon Matsayi
- Xi Jinping Ya Bayar Da Lambar Yabo Mafi Girma A Fannin Kimiyya Da Fasaha Ta Kasar
Bugu da kari, firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kasa da kasa su zurfafa musaya da hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha. Yana fatan kasa da kasa su samar da kyakkyawan yanayi mai adalci ba tare da wariya ba, domin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha bisa kare ikon mallakar fasahohi.
Shugaban dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya Klaus Schwab ya jagoranci taron tattaunawar, inda wakilan masana’antu da cinikayya 200 daga kasashe da yankuna 40 suka halarci taron. (Masu Fassarawa: Zainab Zhang, Fa’iza Mustapha)