Shafin Rumbun Nishadi shafi ne da yake zakulo muku fitattun jaruman finafinan hausa manya da kanan daga cikin masana’antar kannywood, har ma da mawakan da suka shahara ko suke shirin tasowa.
A wannan makon a yau ma shafin na tafe da wani hazikin mawaki, matashi me shirin haskawa a yanzu wato, JIBRIN MUHAMMAD wanda aka fi sani da PRINCESS DABO. Inda ya bayyanawa masu karatu irin kalubalen da ya fuskanta kafin ya fara waka da kuma bayan ya fara wakar, har ma da wasu batutuwan masu yawa.
- Barazanar Da Rashin Katabus Na Kananan Hukumomi Ke Yi Ga Dimokuradiyyar Nijeriya
- Mutane 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Su Da Hannu A Sace Mahaifiyar Rarara
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar mu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Da farko masu karatu za su so su ji cikkken sunanka.
Sunna Jibrin Muhammad wanda aka fi sani da Prince Dabo.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
An haife ni a wani gari mai suna Wadata a Jihar Neja, matsayin karatuna iya sakandare ne.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma fanninn waka waka?
Gaskiya soyayya ce ta yi sanadin fara wakanata, duk da wace nake kauna bata sona amma niz zan zamo mai yi mata addu’a da fatan Alkhairi.
Kamar wacce irin waka k fi mayar da hankali kai?
Kowacce waka ta zo mun na kanyi a matsayina na mawaki, sai dai nafi rera ta soyayya.
Ko akwai wani ko wata da suke rubuta maka waka?
Waka baiwa ce ba wanda yake rubuta mun ita.
Idan na fahimce ka kana so ka ce da.kanka ka fara rubuta ka je ka rera ba tare da taimakon kowa ba, haka ne?
Na nemi taimakon tsohon ubangida na Adam Fasaha, yayi matukar kokari domin ya ga na dan goge a harkar, sai dai ban taba zuwa wajen wani ya rubuta mun waka ba sai dai bayan na rubuta akan gyara mun wasu kalmomin cikinta.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara waka?
Gaskiya na fi shekara goma ina gobzawa da kaina.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Ina waka ne da iya kwarin gwiwa ta, sai dai addu’ar iyaye da taimakon abokaina sune makamashi na.
Ya farkon farawar ta kasance?
Farkon fara wakata kulum ta Allah so nake na ji wani yana jin waka ta, ko’ina duk inda na zo wucewa in ji masoyana suna kiran sunana PRINCE DABO, na sha tura wa mutun waka ta dana bar wajen sai ya goge, sai dai farkon shigata ‘studio’ na ji kunya sosai, sai dai ban ji tsoro ba.
Ka yi wakoki sun kai kamar guda nawa?
Ban san adadin yawan wakokina ba, saboda na yi da yawa.
Ko za ka fadawa masu karatu sunayen wasu daga cikin wakokin da ka yi?
Sunayen wakokina da suka yi fice sosai sune; Majunin Zainab, Dabo Na zo, All The Best, Ina Sonki, Wani Abu Na Zuciya, Za Ta Fashe, Lokaci Na, ‘Yar Shuwa, Prince Dabo Ne.
Wacce irin waka ka fara yi?
Wakar siyasa na fara rubutawa kuma shi na fara rerawa, wacce ta fi karbuwa kuma ita ce (Dabo na zo).
Wane irin nasarori ka samu game da waka?
Waka ita ce silar da ya sa na zauna a kano da zummar cewa watarana zan daukaka, an yi mun alkhairi da dama musamman ‘yan’uwana da abokaina da iyayen abokaina sune nasarata.
Wane irin kalubale ka samu game da waka?
Na fuskanci kalubalai masu yawan gaske kamar haka; Rashin kudi, Rashin magoya baya, Rashin tsayayyen uban gida da kuma karancin kulawa dana samu a rayuwata. Saboda rashin kudin mota na sha takawa daga Hotoro dan’marke zuwa zoo road a kafa, wani lokacin ma bana samun karyawa kuma ko naje studio ba mai siya mun abinci haka nake wuni ba ci sanadiyar alfarma da ake yi mun a ‘studio’, haka nake wuni a ‘studio’ kuma na koma gida a kafa wani lokacin ma sai nayi sati ina zuwa ba mai kula ni, sai dai wasu lokutan na kan roki kudin mashin a wajen al’umma a lokacin da al’umma ke mun dariya a lokacin Allah ke kara mun kwarin gwiwa. Ban samu matsala da iyaye na ba saboda sune masu karamun karsashi, bana jin komai idan wani ya zage ni saboda ina son waka yau ina yin mara dadi gobe zan yi mai dadi fata na kawai masu yi mun dan gani su dawo yi mun babban gani.
Wacce waka ce ta zamo bakandamiyyarka cikin wakokinka?
Bakandamiyar wakata ita ce Yayata.
Me ya ja hankalinka har kayi wakar za ta fashe?
Za ta faahe waka ce dana yi ta domin farin ciki na dana masoyana, gaskiya wakar za ta fashe ta karbu a Jos sosai domin duk wani guy dan wanka yayi yayin wakar.
Kamar da wanne lokaci ka fi jin dadin yin waka?
Gaskiya na fi jin dadin waka ni kadai shi ya sa bana saka mace ko kuma nayi da wani, bana jin dadin waka da kowa na fi son na ga ni kadai a ‘studio’ ta hakan ne kadai nake samun damar bayyana sakon dake zuciya ta.
A baya na ji ka kira sunan Adam Fasaha da tsohon ubangidanka, shin a yanzu wane ne ubangidanka a fannin waka?
Har yanzun ba ni da tsayayyen ubangida wanda zai tafa mun a harkar wakokina tukunna, sai dai da’akwai masu taimaka mun kamar su Brother Yakubu da kuma masu ba ni kwarin gwiwa a cikin abokaina da sauransu.
Mene ne burinka na gaba game da waka?
Buri na shi ne na ga na zama babban ‘celebrity’ kuma ina burin na ga na kafa ‘record’ na taimakon kananun mawaka masu burin su ga sun zama wasu, kuma ina burin na ga wakokin hausa ya za ga duniya kamar na kowane yare.
Ya ka dauki waka a wajenka?
Na dauki waka sana’a, sanan na dauki waka wajen aika sakon zuciya na ga masoyana, kuma abun da zai bani rayuwa mai kyau da girma da daraja a idon duniya wanan shi ne abun da na dauki waka.
Wa ya fi burge ka a cikin mawaka?
Adam zango ya fi burge ni saboda yana taimakon kananun mawaka kuma shi ne Jarumina.
Bayan waka kana harkar fim ko sha’awar shiga cikin masana’antar?
Bana harkar fim kuma bana kida ni kawai mawaki ne.
Bayan waka kana wata sana’ar ne ko tukunna dai?
Gaskiya bana wata sana’a bayan waka.
Wane ne babban abokinka a cikin mawaka?
Babban abokina a mawaka shi ne Sultan Baby, babban makadin Hausa.
Idan aka ce ka zabi mutum daya wanda za ku yi waka tare wa za ka dauka?
Adam A. Zango zan dauka ina son na ga mun yi waka tare.
Ka taba haduwa da Adam A. zango?
Allah bai taba hada mu ba, amma idan zai yi ‘show’ na kanje na kalla kuma ina son Adam Zango ya taimake ni.
Wane kira ka ke da shi ga masu kokarin fara waka?
Kiran da zan yi wa wadanda suke burin fara waka shi ne su zamo masu hakuri, shawarar da zan basu shi ne su rika kula da kalaman cikin wakokinsu domin ita waka sako ce a koyaushe su zamo masu bin umarnin iyayensu.
Wane sako ka ke da shi ga masoyanka?
Sako na ga masoyana shi ne na yi musu alkawarin sai na je inda suke son na je in sha Allah, sako na ga Adam Zango shi ne ina yi masa fatan Alkhairi.
Me za ka ce da wannan gidan jarida ta Leadership Hausa?
Ina yi wa gidan LEADERSHIP Hausa fatan alkhairi na ji dadin kasancewa da ku domin kun cire mun wani abun da ya dade yana damuna a zuciyata, nagode. Masu karanta hirana Allah ya saka muku da gidan Aljena, ina mai kara fada muku cewa duk abun da na fada gaskiya ne ina alfahari da ku.