Babbar Hanya Zuwa Hakar Ma’adanai
Yawan al’ummar Nijeriya a ranar 17 ga Yunin shekarar 2024 ya kai miliyan 228.9, bisa la’akari da sabn bayanan Majalisar Dinkin Duniya na Wrldmeter.
Wannan ya sanya Nijeriya a matsayin ta 6 a yawan al’umma a duniya, inda yawancin alúmarta ke da matsakaicin shekaru na 17.2, kuma kashi 53.9 cikin dari na yawan jama’a suna zaune a birane ne.
- Mutane 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Su Da Hannu A Sace Mahaifiyar Rarara
- Yadda Gidan Buhari Ya Zama Fadar Ziyarar Jiga-jigan ‘Yan Siyasa
A wannan yanayi, Nijeriya na fama da rashin biyan kudaden fansho ga masu ritaya. A shekarar 2022 PenCm ta bukaci da majalisar dokoki da ta bada izini a biya bashin fansho da ake bin gwamnatin tarayya har Naira biliyan 577. Wannan lamari ne mai ban tsoro.
Yayin da ake bin jihhi 21 jimillar Naira biliyan 790 a watan ktban 2023, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito. Allah Madaukakin Sarki ne kadai ya san adadin ma’aikatan gwamnatin tarayya da na jihhi 36 da kananan hukummi 774 da ke bin bashin fansho na shekaru da aka ki a biya su a halin yanzu.
Hauhawar farashin kayayyaki sama da kashi 33 cikin 100, hauhawar farashin kayan abinci sama da kashi 40 cikin 100, inda aka yi hasashen mutum miliyan 31 za su fuskanci karancin abinci nan da Agustan 2024. Kimanin kashi 63 cikin 100 na ‘yan Nijeriya miliyan 133 na fuskantar talauci mai dimbin yawa.
Cire tallafin wutar lantarki tare da samun wutar lantarki mai karfi na kasa da mega watt 4500. Jimlar bashin cikin gida da waje na Naira triliyan121.67 kwatankwacin Dala biliyan 91.46, ya zuwa watan Maris 2024 ake bin gwamnatci, a cewar fishin Kula da Basussuka (DM).
Rashin aikin yi ga matasa a cewar hukumar kididdiga ta kasa ya karu zuwa kashi 7.2 cikin dari. Daga ina k zuwa ina? Da kuma cire tallafin mai tare da sayar da mai akan matsakaicin kudi na Naira701.24 akan kwace lita a watan Afrilun 2024 bisa ga farashin NBS Price Watch.
Akwai babban gibin ababen mre rayuwa amma tare da bada kwangilan gina babbar hanyar Legas zuwa Calabar da ke cin Naira biliyan 4 sabanin Naira biliyan 8 a kowace kilomita a cewar ministan ayyuka. Rikicin al’umma da addini, ‘yan fashi da garkuwa da mutane da ke nuni da gazawan hukuma inda har yanzu ‘yan matan Chibk 90 ba a ji duriyarsu ba tsawon shekaru 10, bayan haka kuma adadin wadanda aka yi garkuwa da su a cikin Nijeriya ya zama wani gaibu.
Kin bayar da tallafin karatu na gida ga daliban Nijeriya da kuma tilasta musu shiga bautar bashi tun kafin su balaga. Rashin magunguna da asibitcin jinya, rashin ruwan sha, barazanar korar ma’aikata da kuma kin karin mafi karancin albashi daga Naira dubu 30, saboda wai rashin isassun albarkatun kasa. Kin samar da kayan kyarwa na yau da kullum a kowane mataki na fannin ilimi da kuma tilasta wa dalibai biyan kudin jarabawar WAEC, NEC da JAMB. Darajar Naira a kan Dala ya yi kasa inda yanzu Dala daya tana kwatankwacin 1,483.91 a kasuwar NAFED da kuma 1,485.53 a kasuwar NAFEM a ranar 20 ga watan Yuni na shekarar 2024. Duk alkalumman da ke da alaka an sam su ne daga bayanan ‘Statisense’ da ta buga bisa alkaluman Ma’aikatar Kudi ta Tarayya a 2024.
Gwamnatin Tarayya da kusan dukkan jihohin kasar na ci gaba da bai wa tsofaffin shugabanninsu marasa kishin kasa fansho na fitar hankali, lamarin da ya kara ta’azzara kalubalen tattalin arzikin a kasa da talakawa ke fuskanta.
Bari mu tsunduma cikin bayanai.
Yanayin Zalunci
A cikin jihhi daban-daban, masu karbar fansho suna fuskantar kalubale masu yawa. Wadannan tsfaffin ’yan kasa da suka sadaukar da shekarunsu na aiki ga aikin gwamnati, a yanzu sun samu kansu cikin mawuyacin hali da matsananciyar wahala da kuma banbance-banbance tsakanin rayuwar ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da kudaden fansho na cuta da tsfaffin shugabannin kasar da munanan dabi’unsu da kuma tsfaffin gwamnni da mataimakansu ke mrewa, ya fit fili kuma yana nuni da sace-sacen albarkatun kasa da masu karancin gaskiya wadanda suka sami kansu a matsayi shugabanni ke yi.
Yayin da ’yan fansho ke fafutukar samun ‘yancinsu da kuncin rayuwa bayan shekaru da dama da suka shafe suna yi wa kasa hidima, su kuwa tsfaffin shugabanni da suka yi aiki na tsawn shekaru takwas kacal suna rayuwa ne cikin jin dadi, kuma suna samun kariya daga fakitin fansho na tfin Ala-tsine.
Dimbin Bashin Fansho da ba a biya ba: Masu karbar fansho suna bin gwamnatin tarayya da na jihohi makudan kudade, wasu tun shekaru da yawa. Duk da yin hidima har na tsawon shekaru 35, har yanzu ba su sami hakkinsu ba. Akwai kukan da ake gani inda wasu suka taru a harabar gidajen gwamnati, rike da allunan da aka rubuta, “Mugaye, ku biya mu fanshoonmu” da kuma “ku ji tsoron Allah, ku biya mana kudadenmu”. Wadannan su ne al’amuran da ke gudana a wasu jihohin.
Kalubalen Rashin Lafiya: Yawancin masu karbar fanshoo suna kwance a gadajen asibit kuma suna fama da cututtuka saboda damuwa da rashin biyan kudinsu na fansho da kuma bashin fansho ke haifarwa. Adadin ‘yan fansho da suka rasa rayukansu suna jiran fansho ya kai daruruwa yayin da wasu daruruwan ke fama da rashin lafiya.
Bude kofar ambaliyar Fansho na cuta
Kundin tsarin mulkin Nijeriya, musamman sashe na 84 (5-6): Ya tanadi cewa duk mutumin da ya rike mukamin shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa, zai iya samun ‘yancin fansho na rayuwa daidai da albashin shekara-shekara na shugaban kasa haka ma mataimakin shugaban kasa.
Dokar mai rike da fishin gwamnati (Biyan Fansho) mai lamba 11 na shekarar 2007 na jihar Legas ita ce ta farko da ta fara aiwatar da irin wannan dokar rashin kan gado ta fansho a shekarar 2007, wadda gwamnan wancan lokaci ya sanya wa hannu makonni kafin ya fice daga wa’adinsa na wa’adi biyu. Dokokin sun ba da fansho na har bayan rayuwa da sauran fa’idoji ga tsohon gwamnan da sauran gwamnni da za su biyo baya.
Akalla jihohi 22 a Nijeriya sun kafa irin wannan la’ananniyar dokar ta fansho da ke da bam mamaki. Daga cikin jihohin akwai Abia, Akwa Ibm, Bauchi, Bayelsa, Borno, Delta, Ebnyi, Edo, Gmbe, Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Imo, Neja, Osun, Ribas, Yobe da dai sauransu. Ko da yake wasu jihohin na cewa sun watsar kuma sun yi bitar su ya zuwa matakan da har yanzu ba su da wani tasiri. Watakila ma rufa ido ne!
A halin da ake ciki kundin tsarin mulkin Nijeriya, musamman sashe na 210 (3) ya yi wa ma’aikatan gwamnati a jihohin Nijeriya alkawarin cewa gwamnatcin jihohinsu za su sake duba kudaden fansho duk bayan shekara biyar. Abin takaici, sun saba wannan alkawarin da suka dauka.
Wannan wace irin al’umma ce?
Fashi da Tsakar Rana
Wadannan dokokin sun ba su kusan hakki iri daya na shagali, wanda kuma gwamnati ce za ta biya, sun hada da:
1. Gina gida ga kowannensu a wuraren da suka fi so a cikin jihohinsu da Abuja. 2. Ba su tsakanin sabbin motoci biyu zuwa shida duk bayan shekaru uku ko hudu. 3. Ba su kashi 100, wuri-na gugan-wuri na ainihin albashin shugaban da ke kan karagar mulki. 4. Kula da lafiya kyauta ga shugaban da iyalansa a cikin gida ko a kasashen waje.
5. Alawus na kula da gida, alawus din kayan aiki, alawus din gyaran sabuwar mota, da alawus na nishadi. 6. Ba su mataimaka na musamman, ‘yansanda, da ma’aikatan ma’aikatar tsaro na DSS har bayan rayuwarsu. 7. Ba su kudin hutun shekara-shekara na kwanaki 30 a ciki da wajen Nijeriya. 8. Za a sake duba wadannan kudade idan aka samu karin albashin shugaban da yake kan karagan mulki da dai sauransu.
Kar ku manta a lokaci da suke kan mulki, kasa da jihohin su ke biya ko da kuwa tsinken sakace ne na cire haramtaccen naman da ya makale a hakorinsu ne.
Tambayata a nan ita ce, me suka yi da suka cancanci irin wannan ganimar da shagali?
Kunnen uwar shegu
Bambance-bambancen da ke tsakanin fansho da tsfaffin shugabannin kasa da gwamnni ke samu da kuma tabarbarewar tattalin arzikin da galibin ‘yan Nijeriya ke fuskanta ya kai fadi da zurfi kamar sama da kasa. Kungiyoyi irin su Kungiyar Kare Hakkkin Tattalin Arziki (SERAP), sun yi kakkausar suka da kuma adawa, inda suka yi ta kkarin ganin an kawo karshen wannan hauka da zalunci.
Shin ina NLC da TUC suke ko sun tattara ne kawai a haukan neman karin albashi?
A shekarar 2019, wata babbar ktun tarayya da ke zamanta a Ikoyi a Jihar Legas, ta umurci gwamnatin tarayya da ta kwato kudaden fansho da tsofaffin gwamnnin da ke rike da mukamin minista da ‘yan majalisar tarayya suka karba.
Me ke Damun Nijeriya?
Abubuwan da ke tattare da kudi suna da ban mamaki. Kudaden fansho da tsofaffin shugabannin Nijeriya, mataimakan shugaban kasa, da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Nijeriya ya kai Naira biliyan 9.2 cikin shekaru hudu. Bugu da kari, Gwamnatin Tarayya ta ware wani Naira biliyan 2.3 don biyan wadannan kudade na fansho a cikin shekarar 2022 kadai.
Kamar yadda bayanai suka fito daga ofishin kula da basussuka (DM) har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2019, kimanin jihohi 26 a Nijeriya da ke da dokar fansho na tsofaffin gwamnnin su ana bin su bashin Naira triliyan 3.92 a cikin gida da waje.
Yarjejeniyar kasa da kasa kan cin hanci da rashawa da dokar da’a
Yarjejeniyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCAC): Ta karfafa gwiwar kasashen mambbin kungiyar da su dauki matakan hana cin hanci da rashawa, ciki har da gudanar da kudaden gwamnati cikin gaskiya da rikon amana.
Ka’idojin ECD na Gudanar da Jama’a: Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki da Ci Gaba (ECD) ta jaddada ka’idoji kamar gaskiya da rikon amana a cikin gudanar da aikin gwamnati.
Ka’idojin da’a na jami’an gwamnati, kamar yadda yake kunshe a cikin sashe na 1 na jadawali na uku da na biyar na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999, ya haramta ma’aikacin gwamnati da yin amfani da mukami na hukuma don biyan bukatun kansa da dai sauransu.
Ina za mu sa gaba?
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (Internatinal Criminal Curtf Justice) ita ce wuri mafi kyau a gare su!