Kungiyar masu hakar ma’adanai ta Nijeriya reshen jihar Neja ta yi kira da a sake duba dokar hana hako ma’adanai da acaba da gwamnatin tarayya ke shirin yi.
Shugaban kungiyar, Alhaji Mohammed Mambo ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka yi a Minna, inda ya ce haramcin zai kara ta’azzara matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa da mata a harkar hakar ma’adanai a kasar nan.
Ya ce dubban matasan Nijeriya da mata ne ke cin gajiyar harkar hakar ma’adanai da kuma sana’ar acaba saboda rashin isassun hanyoyin da za su iya samun hanyar gudanar da rayuwarsu.
A cewarsa, hana hakar ma’adanai da babura ba zai haifar da da mai ido ba kuma zai kara ta’azzara rashin tsaro domin akwai yuwuwar a dauki matasan da dama cikin kungiyoyin masu aikata laifuka.