Alkaluman hukumar gidan waya ta kasar Sin sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yuni, yawan kayayyakin da kasar ta yi jigilarsu cikin sauri ya kai fiye da biliyan 80, kasa da kwanaki 59 wajen kai ga samun wannan adadi bisa na shekarar bara.
A bana, sha’anin jigilar kayayyaki cikin sauri ya samu bunkasuwa cikin sauri, matsakaicin yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu a kowace wata ya kai fiye da biliyan 13. Musamman ma a watan Yuni, yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu ya zarce miliyan 500 a kowace rana saboda rangwamen da kamfanoni suka bayar a tsakar shekara da sauransu. (Amina Xu)