Ƙungiyar Marubuta ta Arewa Media Writers, ta yi kira ga gwamnonin Arewa, da su sake duba matsayin sarakunan gargajiya tare da ƙarfafa matsayin su a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Haidar Hasheem Kano shi ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a babban taron ƙasa da ƙungiyar ta gudanar a Kaduna, ƙarshen makon jiya.
- NAFDAC Ta Yi Bikin Lalata Kayayyakin Jabu Na ₦985.3m A Kano
- Wata Sabuwa: KEDCO Ta Yanke Wutar Jami’ar Dangote Da Ke Kano
Taron wanda ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga jihohi 9 har da Abuja, ya mayar da hankali ne kan batutuwa da suka shafi inganta ayyukan ƙungiyar da duba wasu muhimman al’amura da suka shafi yankin Arewacin Nijeriya, ciki har da taɓa martabar masarautun gargajiya a wasu jihohi da cigaba da taɓarɓarewar tsaro.
Da yake yaba wa ƙoƙarin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da hafsoshin tsaro kan yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar nan, ya bayyana buƙatar su ruɓanya ƙoƙari a fannin, inda ya yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan a garin Gwoza, na Jihar Borno, tare da kiran kada a bari irin wannan mummunan al’amari ya sake dawowa arewacin ƙasar nan.
An kafa ƙungiyar Marubuta ta Arewa Media Writers ne, a ranar 17 ga watan Yuli, 2020 da nufin haɗa kan matasa domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma ta hanyar rubuta rubuce-rubuce.