Hamshaƙin Attajiri kuma Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya yi kakkausar suka kan ƙarin kuɗin ruwa da babban Bankin Nijeriya CBN ya yi wanda ya kai kusan kashi 30 cikin dari.
Da yake jawabi a ɗakin taro na Banquet dake birnin tarayya Abuja, yayin buɗe taron kwanaki uku da ƙungiyar masana’antun Nijeriya (MAN) ta shirya, Dangote ya bayyana illolin da sabon tsarin kuɗin ruwan zai haifarwa wajen rage samar da ayyukan yi da kuma bunƙasar kamfanoni a ɓangaren masana’antu.
- An Tona Asirin Masu Yi Wa Matatar Dangote Zangon Ƙasa
- Wata Sabuwa: KEDCO Ta Yanke Wutar Jami’ar Dangote Da Ke Kano
Dangote ya jaddada cewa idan aka samu kuɗin ruwa na kashi 30 cikin 100, ba zai yiwu a samar da ayyukan yi ko kuma bunƙasa masana’antu sosai ba. Ya buƙaci gwamnati da ta aiwatar da sabbin tsare-tsare da zasu bayar da kariya da raya masana’antu na cikin gida, yana mai nuni da cewa manyan ƙasashen yammaci da gabashin duniya suna kare masana’antunsu sosai don tabbatar da ci gaba da yin takara ragowar kamfanonin ƙetare
“Babu wanda zai iya samar da ayyukan yi da kuɗin ruwa na kashi 30%. Babu wani ci gaba da zai samu,” in ji Dangote.
Ya kuma yi gargadi game da illolin dogaro da shigo da kayayyaki, inda ya kwatanta shi da shigo da talauci da fitar da ayyukan yi zuwa kasashen waje. Kana ya jaddada mahimmancin samar da bashin kuɗaɗe masu rahusar kuɗin ruwa don samun ci gaba, sannan ya danganta rashin kariyar masana’antu da tabarbarewar tsaro, da ƴan fashi, da garkuwa da mutane, da talauci a ƙasar nan.