Wata babbar kotun yanki, ta aike da dalibin makarantar Sakandaren jeka ka dawo, Idris Alex Emeka, gidan yari, bisa samunsa da laifin yi wa wata mahaukaciya fyade har sau uku a Yola.
Babban Kotun Majistaren ta 2, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake ƙarar ne bayan an gurfanar da shi a gabanta bisa laifin fyade.
- Fyade: An Yanke Wa Robinho Zaman Gidan Kaso Na Shekara Tara
- Ana Zargin Wani Hadimin ‘Yar Majalisa Da Yi Wa Almajiri Fyade A Kaduna
Alkalin kotun mai shari’a Musa Alhaji Adamu, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara bayan da ya amsa laifin da ya aikata wanda ya saba wa sashe na 260 na dokar ƙasa.
A cewar mai gabatar da ƙara, an kama dalibin ne mai shekaru 20 ya na kan lalata da wata mata maitabin hankali a ranar 26 ga Yuni, 2024.
A rahoton farko da aka gabatar a gaban kotu, mai gabatar da ƙara ya yi zargin cewa wanda ake tuhuma ya yi lalata da matar maitabin hankali har sau 3 a lukaci guda.
Yayin da yake gurfanar da shi a madadin rundunar ƴansandan jihar, Sufeto Galeon Nimrod, ya shaida wa kotun cewa wani Mutum ne mai suna Habu Jibrilla, ya kawo ƙara ofishin ƴansanda na Karewa.
Sufeto Galeon, ya bayyana cewa Jibrilla a wanda mazaunin Unguwar Lowcost Jimeta ne ya bayyana cewa, ya kama wanda ake ƙara yana lalata da mahaukaciyar a kan titi da karfe 6:40 na safen ranar 26/6/2024.