Cacar baki ta kaure tsakanin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike da Sanata Ireti Kingibe mai wakintar mazabar Abuja a zauren majalisar dattawa.
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), ya sha alwashin cewa Sanata Ireti ba za ta koma zauren majalisar dattawa ba a 2027.
- An Aike Da Ɗan Shekara 67 Gidan Yari Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Mata 2 Fyaɗe Yana Ba Su ₦500 A Bauchi
- Ya Zama Wajibi Amurka Ta Sauke Nauyin Dake Wuyan Ta Game Da Kasar Afghanistan
Ireti ta tsaya takara a jam’iyyar LP, inda ta doke Philip Aduda na jam’iyyar PDP, wanda ya hau kujerar tun daga 2011 zuwa 2023.
Aduda, wanda a fili yake shirin komawa zauren majalisar dattawa, an gan shi yana zagayawa da Wike a yayin rangadin ayyuka.
Da take magana a wani shirin gidan Talabijin na ARISE, ‘yar majalisar ta ce Wike bai tsanana komai ba ga mutanen Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ta ce ayyukan samar da ababen more rayuwa da Wike ya kaddamar ba za su amfanar da talakawa ba, inda ta zargi ministar da rashin nuna damuwa kan warware muhimman batutuwan da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki da suka addabi al’ummar Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ta ce, “Watakila ministar ya kasance minister ne a ma’aikatar da ba ta da jama’a. Sai dai wani yanayi na musamman na ministan Babban Birnin Tarayya shi ne, baya ga samar da ababen more rayuwa da tituna, dole ne ya yi la’akari da bukatun al’ummar wannan yanki. Wannan shi ne ya bambanta shi da ministan ayyuka, ko wata ma’aikatar.
“Ministan Babban Birnin Tarayya yana nuna kansa kamar wani gwamnan. Kamar yadda mutane suka yi min magana a lokacin da aka kaddamar da wadannan hanyoyin. Sun ce, jama’a na murnan bude tituna a Maitama da kuma Gundumar Abuja ta Tsakiya, yawancin jama’a ba sa zama a wurin. Ba zai iya nuna wani aikin da mutane za su amfana kai tsaye a wuraren da suke zaune.
“Bambancin kenan, kamar dai gwamna ya ce maka ya gina wasu hanyoyi, don haka bai damu da bukatun mutane ba. Su mutanen Abuja suna da bukatoci da ya fi na hanyoyi. Domin al’ummar garin Abuja na fama da rashin ruwa, wutar da sauran abubuwa.”
Da yake mayar da martani, Wike, ya ce ba ya ofis ne don ya faranta mata rai, inda ya kara da cewa ya yi ayyuka masu muhimmanci cikin kankanin lokacin da aka nada minista.
Ministan ya ce sanatan Abuja za ta rasa goyon bayan mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja a zaben 2027 mai zuwa.
Wike ya ce, abin takaici ne a ce maimakon ta hada kai da shugabancinsa, amma ta ki yin haka inda ta koma baya tana sukar ayyukansa da na Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Ya ce: “Na ji wani shiri a gidan talabijin na Arise TB a safiyar yau. Sai dai kash, ina jin yar majalisar dattawa ce ta fadi haka, kuma abin takaici ta fadi. Tare da girmamawa, abin da ba ka sani ba, ba ka sani ba, abin da ka sani, ka sani.
“Ta ce babu asibitoci kuma akwai. Ke a matsayinki na ‘yar majalisa me ka yi? Nawa kika tallafa mana don inganta fannin ilimi da lafiya?
“Ina kalubalantar sanatan Abuja da cewa, ba za ta dawo wannan kujerar ba a zaben 2027, domin ta rasa magoya baya masu yawa.”
Bayan wannan martini ne, sanadar Abuja ta bayyana cewa Wike bai da kuri’a ko daya a Babbar Birnin Tarayya ballantana ya hana ta sake dawowa wannan kujera.