Kasar Ingila wadda ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar EURO da aka buga shekaru biyu da suka gabata, ta samu tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe bayan ta fitar da kasar Switzerland a bugun Fenareti.
Embolo ya fara jefa wa Switzerland kwallo a ragar Ingila kafin Bukayo Saka ya farke wa kasar tashi a minti na 80.
- Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?
- Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Kan Aikin Tinkarar Ambaliyar Ruwa A Kasar Sin
Bayan kammala minti 90 na farko ne alkalin wasa, Daniele Orsato, ya kara mintuna 30 na karin lokaci amma duk da hakan duka kasashen biyu suka kasa fidda kitse daga wuta.
Hakan ya sa aka yi bugun daga kai sai mai tsaron raga, wanda Ingila ta lashe da ci 5-3.