Firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya gabatar da sako zuwa ga Keir Starmer a yau Lahadi 7 ga wata, don taya shi murnar zama firaministan kasar Birtaniya.
Li ya ce, Sin da Birtaniya, zaunannun membobi ne a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kana, manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. Yana cewa inganta mu’amala da hadin-gwiwa tsakaninsu, ya dace da muradunsu, kuma zai taimaka ga inganta hadin-gwiwar kasa da kasa wajen shawo kan kalubalen duniya.
A cewarsa, gwamnatin kasar Sin na maida hankali sosai wajen raya dangantakar dake tsakaninta da Birtaniya, tana kuma fatan yin kokari tare da sabuwar gwamnatin Birtaniya, don karfafa samun fahimtar juna ta fannin siyasa, da habaka hadin-gwiwa, da inganta mu’amalar al’adu, don taimakawa ga ci gaban tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’umma, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a duniya baki daya. (Murtala Zhang)