An buɗe gasar kwallon kafa ta cin kofin baban Hafsan Sojojin Nijeriya a Katsina domin taya shi murnar cika shekara ɗaya a ofis.
An shirya gasar ne da nufin ƙara kyautata alaƙa a tsakanin matasa, inda kulob 32 za su fafata a filin wasa na birget na 17 da kuma filin wasa na KCK da ke Katsina.
- Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki, Sun Yi Kisa, Sun Kwashe Mutune 22 A Katsina
- Jami’ar ‘Yar’aduwa Ta Katsina Ta Kama Hanyar Rugujewa – ASUU
Tunda farko da yake jawabi a taron bikin buɗe gasar, baban kwamanda mai kula da Birget na 17 da ke Katsina, Ibikunle Ademola Ajose, ya bayyana cewa shirya irin waɗannan wassani abu ne mai kyau, domin ta haka ne za a ƙara kulla alaƙa a tsakanin matasa.
Ya ƙara da cewa waɗanda suka shirya wannan gasa sun yi hangen nesa, kuma sun yi abin da yakamata a lokacin da ya dace, musamman don tunawa da shi babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Christopher Gwabin Musa
.
A cewar baban kwamanda mai kula da birget na 17, Ibikunle Ademola, yana fatan za a yi wannan gasa a kammala cikin nasara ba tare da wata matsala ba, musamman tun da abin ya haɗa da matasa.
A wajen wannan biki dai kungiyoyin kwallo guda biyu ne suka kara, wato Sarkin Yaki da kuma K-Soro, wanda bayan an fafata daga ƙarshe kungiyar kwallon kafa ta K-Soro ta samu nasara da bugun daga kai sai mia tsaron gida.
Yanzu dai za a ci gaba da waɗannan wassani a filin wasa na KCK, inda ake sa ran sauran kolab ɗin za su nuna bajintar su domin samun nasara a ƙarshen gasar.
A nasa jawabin, shugaban shirya wannan gasa domin taya baban Hafsan Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, Malam Lawal BK ya bayyana cewa sun yi tunanin shirya gasar ne domin sada zumunci a tsakanin matasa.
Ya ƙara da cewa yanzu hanya mafi sauki da za a ja matasa a jiki, ita ce shirya irin wannan gasa, ya ce babu komai za a ɗora matasa a wata turba wadda za ta hana su yin tunanin abubuwa marasa kyau.
“Matasan mu yanzu idan ka kyale su, ba zamu yi tunanin irin wanda yakamata ba, amma shi wasan ƙwallon ƙafa abu ne da matasa ke so, to ko ba komi ka ɗebe masu kewa sannan ka sanya su nishadi ” inji shi
Kamar yadda aka tsara kungiyoyin kwallo kafa guda 32 ne za su fafata kuma wasa daya ne za a riƙa bugawa duk wanda ya samu nasara zai hau mataki na gaba.
Kazalika an ware kyaututtuka masu yawa wanda a ƙarshen gasar za a rabawa kungiyar da ta samu nasara.
Sauran kungiyoyin kwallon kafar da za su taka leda sun haɗa da Katsina Boys da Shooting Star da Durbi Strikers da KKT Strikers da Home Boys da Gawo Prof. da kuma Kamuwa United da Manaco ATC da dai sauransu.