Wani matashi mai suna Shu’aibu Alhaji Yusuf ya yi barazanar faɗowa daga tsanin gidan rediyon Aso da talabijin dake kan tsaunin Katampe a Babban Birnin Tarayya (FCT) a yau Litinin, matuƙar idan Gwamnatin Tarayya ba ta dawo da tallafin mai da kuma magance matsalolin tsaro a Nijeriya ba. Yusuf, wanda ɗan asalin Maiduguri ne a Jihar Borno, ya bayyana buƙatunsa a rubuce a kan wata kwalba kafin ya hau saman tsanin.
Yusuf ya buƙaci a ayyana dokar ta baci a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina, Kaduna, Neja, da Borno saboda rashin tsaro, yana kira da a ɗauki matakin gaggawa don kawar da ‘yan ta’adda a yankunan. Har ila yau, ya nemi gwamnati ta buɗe kan iyakoki domin shigo da abinci don yaƙar karancin abinci da kuma magance ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta.
- ’Yan Daba Sun Yi Wa Wata Tsohuwa Mai Shekaru 60 Kisan-Gilla A Bauchi
- Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Minista Da Sanatar Abuja
Yusuf ya bayyana cewa ya shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa don waɗannan dalilai kuma ya ƙarfafawa wa ‘yan Najeriya su haɗe da shi a wannan zanga-zanga. Wannan matakin ya jawo hankalin Mrs. Florence Dawon Wenegieme, Muƙaddashin Darakta Janar na Hukumar Kula da Yanayi ta FCT (FEMD), wadda ta tabbatar masa cewa za a isar da korafe-korafesa ga Shugaba Bola Tinubu.
Wenegieme ta yaba da kishin Yusuf kuma ta ƙarfafa masa gwiwar ya ci gaba da kasancewa da rai domin ba da gudummawa da shawarwari don inganta ƙasar. Bayan waɗannan tabbacin, Yusuf ya amince ya sauko daga tsanin, amma nan take ‘yan sanda suka kama shi bayan ya sauko.