Ana kuma sa ran shugaban kasar zai gana da gwamnonin jam’iyyar APC bayan ya dawo daga tafiyarsa a ranar Juma’a domin cimma matsaya daya gabanin babban taron jam’iyyar na kasa na musamman.
Idan zaku iya tunawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnonin a ranar Talata kafin ya tafi kasar Spain domin ziyarar aiki.
- Osinbajo Ya Gana Da Shugaban APC, Abdullahi Adamu Da Wasu Gwamnonin APC 5
- Lokaci Ya Yi Da Nima Zan Zama Shugaban Kasa, Na Gaji Da Yi Wa Wasu Hidima —Tinubu
A daren ranar Alhamis, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gana da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, da wasu gwamnonin APC biyar.
Taron dai ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
LEADERSHIP ta gano cewa taron ba zai rasa nasaba da zaben fidda gwani na shugaban kasa da jam’iyyar zata gudanar a ranar Litinin mai zuwa ba.
‘Yan Nijeriya da dama na tsokaci kan wanda Jam’iyyar zata fitar a matsayin dan takararta na shugaban kasa, wasu na ganin Jam’iyyar zata juya wa Tinubu baya ta rungumi Osinbajo, wasu kuma na ganin Tinubun ba shi da sa’a a zaben cikin kaf masu zawarcin kujerar.
A gefe guda kuma na lissafin cewa tsohon shugaban kasa, Jonathan na iya nasarar karbe tikitin Jam’iyyar, wasu kuma na kallon tsakanin Ameachi da Ahmad Lawal Jam’iyyar zata tsayar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp