Fadar shugaban kasa ta mayar da martani game da kalaman shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, cewa shugaba Tinubu ne ke goyon bayan Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, a rikicin masarautar jihar da ake yi tsakaninsa da Muhammadu Sanusi II.
Mai taimaka wa Shugaba Tinubu, kan yada labarai, Abdu’aziz Abdul’aziz ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin.
- Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Masu Bayyana Ra’ayoyi Suka Zargi Nuna Fin Karfi Da Amurka Ta Yi A Harkokin Intanet
- Gwamnan Zamfara Ya Samu Lambar Yabo Kan Ƙirƙiro Ayyukan Ci Gaba
Ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu na da alaka mai kyau da duka bangarorin biyu musamman Muhammadu Sanusi II.
Ya ce zargin da shugaban na NNPP ke yi ba shi da tushe.
“Abin da mai maganar bai sani ba ko kuma bai fada ba saboda siyasa shi ne; shugaban kasa na da alaka mai kyau da duka wadanda ke takaddama a kan wannan sarauta,” in ji shi.
“Musamman ma Sarki Sanusi II, wanda suke da alaka tun lokacin da ya nemi sarautar a 2014. Kuma ya sani cewa Sarki Aminu Ado bai taba zuwa ya ga Bola Tinubu a fadar shugaban kasa ba tun lokacin da ya hau mulki.”
AbdulAziz, ya ce duk masu irin wannan tunanin su daina, domin Tinubu ba shi da hannu a rikicin masarautar Kano da ake yi a yanzu, face son rai ne na ‘yan siyasar jihar da ke neman tada zaune tsaye.