Al’ummar unguwar da ke Æ™aramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, suna cikin fargaba bayan da Kura ta tsere daga kejinta a gidan ajiyar namun daji da ke yankin.
Kamar yadda rahotonni suka tabbatar lamarin dai ya faru ne tun a ranar Lahadi, wanda ana sa ran dabbar ba ta yi nisa da harabar gidan ajiyar namun dajin ba saboda girma da wajen ke da shi.
- Rikicin Masarautar Kano: Tinubu Da Sanusi II Suna Da Alaka Mai Karfi – Fadar Shugaban Kasa
- Hukumar Tsaron Yanar Gizo Ta Kasar Sin Ta Fayyace Wani Shirin Yaudara Na Amurka
Babban Manajan hukumar yawon bude ido ta Jihar Filato, Chuwang Pwajok, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da shaida wa mazauna yankin cewa su kwantar da hankalinsu domin ana kokarin gano inda dabbar ta shiga don dawo da ita kejinta.
Kazalika ya ƙaryata raɗe-raɗin da ke yawo na cewa yunwa ce ke sanadin tserewar dabbobin wanda ya ce wasu kejin ne sun tsufa amma gwamnati ta ɗauki matakan zamanantar da su nan ba da jimawa ba.
Idan ba a manta ba a shekarar 2015 wani zaki ya taɓa tserewa daga kejinsa a cikin babban gidan namun dajin na Jos.