Wata shaidar masu gabatar da ƙara a shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, a jiya Talata ta bayyana wa babbar kotun tarayya da ke Legas, yadda Emefiele ya yi amfani da kamfanoninsa wajen karɓar kwangiloli da dama daga babban bankin.
Shaidar Ifeoma Ogbonnaya, wacce manajan huldar kasuwanci ne ta bankin Zenith plc, ta shaida wa alkalin kotun, Mai Rahman Oshodi, cewa kamfanonin su ne Limelight Multidimensional Ltd da Come Support Services Ltd da Ambswin Resources Ltd da kuma Magofarm.
- Mun Ja Hankalin Tinubu Kan Tsadar Kayan Abinci – Ndume
- Tsaro Da NATO Take Magana Ya Dagora Ne Kan Salwantar Tsaron Sauran Mutane
EFCC, ta zargi Emefiele da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan aikinsa wanda hakan ya saɓawa dokar cin hanci da rashawa ta 2000, inda shi kuma wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Ogbonnaya, wanda ita ce mai bayar da shaida ta biyar, ta bayyana wa kotun cewa, ba ta taba yin mu’amala kai tsaye da tsohon gwamnan CBN ba, amma tana karbar umarni daga uwargidansa Margaret Emefiele, ta tura kudaden da CBN ke yi zuwa asusun kamfaninsu mai zaman kansa da bankin Zenith.
Ta kuma shaida cewa, baya ga uwargidan Emefiele, ta samu umarni daga wasu mutane biyu John Ogah da Opeyemi Oludimu, da ke aiki da Emefiele, ta hanyar saƙon yanar gizonta, kuma a wasu lokutan ta hanyar kiran waya.
Daga ƙarshen zaman an ɗage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Yuli, domin ci gaba da shari’ar.