A ranar Alhamis ne ake sa ran shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da matarsa, Hafsat da wasu mutane shida za su gurfana a gaban wata babbar kotun jihar Kano, bisa tuhumar su da laifin cin hanci da rashawa da karkatar da wasu kudade.
Gwamnatin Jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP, ta shigar da kara a gaban mai shari’a Amina Adamu Aliyu.
- Nan Ba Da Jimawa Ba Makiyaya Za Su Ci Gaba Da Jigilar Dabobbi A Jirgin Kasa – NRCÂ
- Kaf Nijeriya Cikin Filayen Jiragen Sama Fiye Da 22, 3 Ne Kacal Ake Cin Riba – FAAN
A ranar 5 ga watan Yuni ne, kotun ta bayar da izinin buga sammacin wadanda ake kara, wanda aka yi hakan a ranar 6 ga watan Yunin 2024 a jaridun Daily Trust da The Nation.
Wadanda ake karar sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprisea.
A ranar da aka dage sauraron karar Nuraini Jimoh (SAN) ne, kadai ya wakilci wanda ake kara na shida a kotu a matsayin lauya, amma sauran wadanda ake kara ciki har da Ganduje ba su tura an wakilce su ba.
Alkalin kotun, Mai shari’a Amina Adamu, ta sanya ranar 11 ga watan Yuli domin sauraren karar.