Majalisar dattawa ta samu takardar bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari a hukumance na tabbatar da sunan Mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban alkalin alkalan Nijeriya (CJN).
Bukatar na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata, Litinin 25 ga watan Yuli, 2022, wacce kuma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta a farkon zaman majalisar a ranar Talata.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa nadin da shugaban Kasa Buhari ya yi wa Mai Shari’a Ariwoola a matsayin mukaddashin Alkalin alkalan, ya biyo bayan murabus din tsohon Alkalin Alkalan Nijeriya Muhammad Tanko ne yayi a ranar 27 ga watan Yunin 2022.
Murabus din Tanko dai ya biyo bayan zanga-zangar da wasu alkalai 14 suka yi ne kan korafin su na cewa, wai Tanko ya hana musu hakkokin su na walwala.
Sai dai kuma, tsohon Alkalin alkalan, a cikin wasikar dalilin murabus din nasa, ya bayyana cewa, yana fama da jinya ne.