- Yadda Turawa Suka Fara Haddasa Mana – Masanin Tarihi Usman Dalhatu
- Babu Batun Tsige Sarkin Zazzau
Wani Masanin Tarihin Masarautun Gargajiya da Diflomasiyya a Jihar Kaduna, Alhaji Usman Dalhatu ya bayyana cewa; cire sarakuna wata babbar masifa ce da ke fuskantar Arewacin Nijeriya, duk da cewa irin wannan rikici ba wani sabon abu ba ne, lamarin ne wanda ke da asali tun a lokacin Turawan mulkin mallaka.
Dalhatu, wanda marubucin tarihi ne; sannan kuma makusanci ga marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris ya bayyana cewa; muddin gwamnoni suka ci gaba da yi wa masarautun gargajiya karen-tsaye, ko shakka babu sun dauko hanyar ruguza Arewacin Nijeriya, musamman ganin yadda sarakunan ke bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da kuma hadin kan al’umma baki daya.
Marubucin Tarihin ya bayyana haka ne, a zantawarsa da wakilinmu a Kaduna; inda ya fara da shimfida kan tarihin rikicin sarakunan da kuma Turawan Mulkin Mallaka.
“Wannan rikici na masarautun gargajiya da gwamnoni, bala’i ne da ke shafar Arewa a halin yanzu, wanda Turawan Mulkin Mallaka suka haddasa shi.
“A wancan lokaci, ayyukan da duk sarakuna ke yi; su ne Turawa suka kwace daga hannunsu, suka mayar da sarakunan karkashin gwamnan lardi a halin yanzu. Wannan shegantaka da gangan Turawa suka yi ta, saboda sun samu sarakunanmu da abin da ake cewa, (Well Define System of Gobernment), muna da majalisun dokoki; muna da na zartarwa, muna kuma da na bangaren shari’a, wanda duk duniya da shi ake amfani a lokacin mulkin dimokuradiyya, in ji shi.
Har ila yau, “Turawa sun fahimci muna da ilimin addinin Musulunci, wanda sun samu malamanmu wadanda suka amsa sunansu na malamai a kowane wuri, akalla guda dubu biyu; wadanda sun fi karfin farfesa guda daya da ke Kasar Ingila, sai suka ga idan har suka kyale mu da wannan tsari; ci gaban da za mu samu a duniya ba kadan ba ne, sai kawai suka fito cikin hikima da dabara.
“Tafiya na tafiya, sai suka rika kafa wa sarakuna ka’idoji; duk wanda bai ba su goyon baya ba, sai suka rika amfani da karfin gwamnati suna tuge su har aka zo mulkin jamhuriya ta daya, lokacin da Sa Ahmadu Bello ya zama Firimiyan Kasar Arewa; a wancan lokacin abubuwa da dama sun taso wadanda suke cikin Gwamnatin Sardauna, ‘yan boko ne ‘ya’yan talakawa; wadanda babu wanda suke jin haushi kamar sarakuna; an ba su matsayin minista, sun yi Yes da No; sai suka yi amfani da wannan dama wajen cin mutuncin sarakunan.
“A wancan lokaci a nan Zariya, akwai Malam Jafaru Dan Isiyaku, wanda Allah ya taimake shi har ya gama mulkinsa bai samu matsala ba, suka zo suka yi da Sarkin Zazzau Aminu duk da cewa, sun kafa masa kwamitin bincike; ko da aka yi binciken ba a same shi da wani laifi ba ko kadan.
“Idan ka dauki Kano, Sarki Sanusi dama shi abokin Sardauna ne, wanda shi ne daga baya aka kafa masa wannan kwamiti na bincike, wanda wani Bature mai suna DGM ya shugabanci kwamitin suka ce, sun same shi da abin da ake kira (Financial Irregularity); aka yi amfani da wannan aka tursasa shi ya yi murabus,” in ji Alhaji Dalhatu.
Ya ci gaba da bayyana cewa, “Aka zo kan Sarkin Gwandu, Haruna Rasheed kawunnensa wadanda suka nemi sarautar tare ya samu nasara a kansu ya zama Sarki, su goma sha shida ne wadanda ke ganin sun cancanci zama Sarkin; ba shi ba, haka nan shi ma aka kafa masa wannan kwamiti na bincike; Allah cikin ikonsa ya taimake shi aka kammala binciken ba tare da an same shi da wani laifi ba, tun daga wannan lokaci; ‘yan siyasa suka fara cin mutuncin sarakuna har zuwa lokacin mulkin soja, kafin sarakuna suka dan samu sassauci; saboda bayan su Sardauna, Ironsi ya hau mulki; inda ya yi yunkurin ganin bayan
sarakunan, amma Allah bai ba shi iko ba; domin kuwa wata shida kacal ya yi Gowon ya karbi ragamar mulkin a hannunsa, ya zauna lafiya da sarakunan duk da cewa, akan dan samu tashin-tashina; sakamakon cewa duk wani abu da zai taba martabar addini, ba sa taba yarda a zo da shi; haka aka zo har zamanin Murtala, wanda shi ma bai jima ba haka har zuwa jamhuriya ta biyu lokacin mulkin Shagari.
“A wancan lokaci a Jihohin Kaduna da Kano, gwamnatin PRP ce, inda tsohon Gwamna Abubakar Rimi da Balarabe Musa suka rika yin kalamai masu zafi a kan sarakunan, musamman
Rimi a Kano, wanda ya yi kokarin cin mutuncin Sarkin Kano Ado Bayero, inda kuma su Kanawa suka ga cewa ba za su kyale a rika cin mutuncin sarkin ba. Nan ne aka yi rigima har aka kashe mai ba wa gwamna shawara ta fuskar siyasa, Bala Mohammed; wanda shi ne Maigidan Hajiya Naja’atu.”
Bugu da kari, masanin tarihin ya ce Rimi ya yi amfani da damar da yake da ita wajen kirkirar sabbin masarautu a lokacin, daga cikin masarautun da ya yi; wasu na da Tarihi, wasu kuma ba su da shi. Sannan kuma, bai yi doka a kan masarautun ba; sai abin ya koma wani abu daban na siyasa, “ko da aka canza Gwamnatin Rimi, Sabo Bakin Zuwa ya hau; hawansa ke da wuya ya rushe wadannan masarautu, sakamakon cewa da ma ba a samar da doka wajen yin su ba, saboda haka; har bayan juyin mulkin Buhari ba a samu wani tashin hankali ba kwata-kwata.
“Yanzu kuma da muke cikin jamhuriya ta hudu, sai iya shegen ya fi na kowane lokaci. A lokacin Gwamnatin Rabi’u Kwankwaso, ya nemi ya ci mutuncin Sarkin Kano, Ado sai Allah ya tsare masa mutuncinsa, wanda a karshe matsalar da suka samu ita ce, nadin Wazirin Kano, wanda wannan dalili ake ganin shi ne har ya sanya wa Ado lalurar ciwon zuciya.
“Bayan rasuwar Sarkin Kano Ado Bayero, masu zaben Sarki sun zauna su ga shin wane ne ya fi cancanta, inda suka gabatar da sunayen wadanda suka fi cancanta a wancan lokaci, inda suka zabi babban Dan Sarkin Kano Ado, wanda ke rike da Sarautar Ciroma; inda a lokacin kuma shi Kwankwaso ke ganin cewa, akwai matsala tsakaninsa da Ado Bayero; sakamakon ganin yadda ya nuna wa Malam Ibrahim Shekarau goyon baya, sai ya kullaci Sarkin Kanon duk da cewa; ba ya raye kawai sai ya sauke matsalar a kan ‘ya’yansa, sai aka dauki Sanusi Lamido Sanusi saboda wata manufa ta siyasa ta daban; masu zaben Sarki suka zabe shi, Kanawa kuma kamar a yi tashin-tashina; amma dai aka kyale aka sa ido.
“Sarauta aba ce wacce ke son dabi’u managarta. Na farko rashin yawan Magana, wanda shi ne dalilin da ya sa Sarki yake saka Amawali a bakinsa; na biyu ana bukatar mutum wanda yake da zati; na uku kuma ana son mutum mai kamewa.
“Bayan zaben shekarar 2015, Buhari ya zama Shugaban Kasa; Ganduje kuma ya zama Gwamnan Jihar Kano, ana cikin tafiya sai shi Sarki Sanusi ya rika sukar sa; ai ka ga kuwa ba za su taba zama lafiya ba, wanda ni na san sarakuna da dama sun yi kokarin daidaita wannan al’amari, amma abin ya ci tura; Sarkin Gwandu da bakinsa ya fada min irin kokarin da suka yi wajen daidaita al’amarin, ana cikin hakan ne sai Ganduje ya bai wa wadannan masarautu matsayinsu na asali, sabuwa daga cikinsu kadai ita ce ta Bichi.
“Abu na farko a nan shi ne, Ganduje na son ya rage wa Kano cunkoso ne, abu na biyu kuma wadannan masarautu sun fi Kano dogon Tarihi; dalili na uku kuma shi ne a samu ci gaba ta fuskar tattalin arziki, wannan dalili ya sa ya yi doka sannan kuma aka bi ka’idojin da suka kamata tare da tabbatar wa da wadannan masarautu matsayinsu na asali, ban da Bichi wadda aka kirkira sakamakon ganin tana kusa da Kano, domin rage wa Kanon cunkoso.
“Ina so mutane su fahimci cewa, wannan abu ba a Kano aka fara yin sa ba. Alal misali, a Zazzau idan ka dauki masarautun da ke Jihar Nasarawa; duk suna karkashin Masarautar Zazzau ne, akwai Keffin Dan Yamusa; wanda shi Wakilin Sarkin Zazzau ne a Keffin, inda duk wani Sarki daga Zariya ake nada shi; haka nan idan ka dauki garuruwan Doma da Nasarawa duk suna cikin ikon Zazzau ne, sai bayan Turawa sun ci su da yaki ne suka ba su matsayinsu na cin gashin kansu; suka cire su daga Zazzau, a wancan lokaci babu wanda ya ce abin da aka yi ba daidaita ne ba.
Har ila yau, “Idan ka dauki Masarautar Kauru da Lere da kuma Jere, duk wurare ne da suke da dogon Tarihi; sannan kuma duk suna da tambari, lokacin Gwamna Makarfi ya ba su matsayinsu na asali; su ma ai ka ga daga Zazzau babu wanda ya ce uffan, kuma babu wani gwamna da ya ce; bari ya sauke wadannan masarautu, wanda kuma bisa adalci duk wadannan masarautu sun ci gaba ne saboda na san lokacin da marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris, idan taro ya tashi a Sakkwato ya kan kira Sarkin Lere ya wakilce shi, ko Sarkin Kauru ko kuma na Jere.
“Amma a Jihar Kano, sai aka wayi gari an yi doka yau; an cire Sarki yau; baya ga kuma Sarkin da aka ce an cire shi an bi doka wajen nada shi, wanda masu zaben Sarki suka zabe shi; amma haka kawai sai a ce an cire shi.
“Wannan wuta da tashi a Kano, gobara ce da za ta iya cinye dukkanin Masarautun Arewa baki daya, sannan kuma wannan lissafi ne na miyagun ‘yan siyasa daga Arewa; masu son ruguza Arewar, wanda kuma wannan wata masifa ce da za ta cinye iya kanta gwamnatin. Dalili kuwa, ka taba ji a Kasar Yarbawa ana yin irin wannan? A bangaren Inyamurai fa, ka ji suna irin wannan? Wasu kabilun da ba su kai mu Tarihi ba ma ka ji suna irin wannan? A’a, sai Malam Bahaushe.” In ji shi.
Haza zalika, da yake yin bayani dangane da yadda sarakunan ke shiga lamuran siyasa, ya bayyana hakan a matsayin silar musguna wa masarautun gargajiyar inda ya ce “Gaskiyar magana, babu yadda za a yi aarki ya ki bin umarnin gwamna; dole wanda yake kan mulki da shi za su yi aiki. Saboda haka, ya kamata jama’a su yi wa sarakunan adalci, idan har ana son sarakunan su dawo matsayinsu na asali, ka da wani dan siyasa ya kara zuwa wurinsu da sunan goyon baya ko neman kuri’a; sannan kuma da yawa sarakuna na tsaka-tsaki ne, sai dai a dauki karan tsana a dora musu.
“Saboda haka, sarakuna ba sa shiga cikin harkokin siyasa. Ina mai tabbatar maka cewa, inda sarakuna za su rika shiga harkokin siyasa a Jihar Kano, da jam’iyya mai mulki ba za ta samu nasara ba.
“Kuma muddin ana son samun daidaito a tsakanin gwamnoni da Sarakunan Gargajiya, sai gwamnoni sun janye hannunsu daga cikin harkokin sarakuna, muddin gwamnoni suka dauki nauyin nada Hakimai da Dagatai; an dauko hanyar rusa Masarautun Gargajiya na Arewacin Kasar nan baki daya.” Ya bayyana.
Da yake bayani a kan rahotannin da suke yawo na cewa, an fara samun takun saka tsakanin Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da Gwamna Uba Sani; Alhaji Dalhatu ya ce, “Mun san dai Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so, wanda a yanzu Ahmadu shi ne ke mulki ko an bi hanyar da ta dace ko ba a bi ba, Allah ya kaddara sai ya yi wannan mulki. Don haka, mu mutanen Zazzau, mutane ne masu ilimi da Tauhidi; sannan kuma shi Gwamna Uba Sani, ba dan iska ba ne; ya san irin tarbiyyar da ya taso da ita a gidansu, wanda mu a iya saninmu; babu wata matsala a tsakaninsu,” in ji shi.
…Majalisar Koli Ta Musulunci Ta Yi Kashedi A Kan Rashin Girmama Sarkin Musulmi
Shugabannin al’ummar Musulmin Nijeriya sun gargadi shugabannin siyasa da hukumomin kasar da su rika girmama sarakuna da ba su darajar da ta kamata.
Shugabanin a karkashin inuwar Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) sun yi wannan kashedin ne bayan kammala taron babban kwamitinta na (GPC), wanda babban sakataren kungiyar Farfesa Is-hak Oloyede ya jagoranta a ranar Talata, 2 ga Yuli, 2024.
NSCIA, a cikin wata sanarwa mai dauke da kudurori 11 da sa hannun babban sakataren kungiyar, Farfesa Is-hak Oloyede bayan taron kwamitin nata wanda fitattun sarakunan gargajiya suka halarta, ta bayyana cikakkiyar gamsuwa da kwarin gwiwa ga shugaban kungiyar kuma mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, bisa kyakkyawan jagoranci da sadaukar da kai ga Musulunci da al’ummar Musulmin Nijeriya.
Majalisar ta yanke shawarar kare Sarkin Musulmi daga duk wani nau’i na ‘rashin mutunci’ daga shugabannin siyasa da gwamnatoci, inda ta nanata cewa duk wani rashin mutuntawa ga Sarkin Musulmi, cin zarafi ne kai tsaye ga addinin Musulunci da mabiyanta a Nijeriya.
“Majalisar gudanarwar NSCIA tana ba da shawara mai karfin gaske ga gwamnati da shugabannin siyasa a kowane mataki da su ci gaba da girmama sarakuna da kiyaye mutuncinsu, musamman ma sarakunan da suke da shugabanci na addinin Musulunci don tabbatar da kare al’adunmu da na addini domin dorewar zaman lafiya da ci gaban kasa.
“Al’ummar Musulmi a Nijeriya, tun kafin samun ‘yancin kai, baki daya sun kuduri aniyar yin mubaya’a ga sarakunan addini wadanda za su rika ba da umarni (kan harkokin addini), a kan wannan ya kamata kowa da kowa ya ga kima da mutuncinsu.
“Don haka ya zama wajibi ga masu kula da al’amuran sarakunan su rika nuna girmamawa ga Musulunci ta hanyar ayyukansu da kalaman da suke furtawa saboda al’umma. Duk wani rashin girmamawa ga sarakuna cin zarafi ne kai tsaye ga musulunci da musulmi, ”kamar yadda wani bangare na sanarwar ya ruwaitoare.