Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC Ltd.) ya danganta matsalolin karancin man fetur da ake a Babban Birnin Tarayya Abuja da wasu sassan kasar nan kan matsalar katsewar jigila sakamakon ambaliyar ruwa da wakkiya da ake samu a daminan bana.
Babban jami’in yada labarai na kamfanin, Mista Olufemi Soneye, shi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin da ke bayani kan matsalolin dogon layi da ake samu a gidajen mai.
- Kamfanin Kasar Sin Na Bayar Da Gudummawar Gani Wajen Bunkasa Kasar Najeriya
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-Zirga Ababen Hawa
Ya ce matsalar jigila daga manyan tashoshin kwaso mai zuwa kanana sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a baya-bayan nan shi ne musabbabin wannan matsala.
Soneye ya kuma ce rashin kyawun yanayi ya shafi hada-hadar jiragen ruwa, man-yan tankokin jigila, da kuma jigilar kayayyaki zuwa gidajen mai da suke sassa daban-daban na kasar nan, wanda hakan ya janyo cikas ga aikin samar da kayay-yakin ga gidajen mai.
“Kamfanin NNPC na son yin bayanin cewa saboda gudun tashin wutar fetur da kuma bin umarnin hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NIMET), hakan ya sanya ba za mu iya lodin man fetur a yanayin amfani da walkiya ba.
“Bin wadannan dokoki da ka’idojin sun zama mana dole, duk wani tirjiya ga wadannan ka’idojin ka iya sanya a samu hatsari a cikin rayuwar mutane, motoci da gidajen mai.
“Matakin ya zama babban matsala ga jigilar motocin lodi daga wurin dibo mai zu-wa Babban Birnin Tarayya Abuja.
“Kamfanin NNPC Ltd, na aikin hadin guiwa da hukumomi da masu ruwa da tsaki wajen shawo kan matsalar kayan aiki da kuma yadda za a kauce wa mambaliyar ruwan domin ci gaba da jigilar mai a wuraren da lamarin ya shafa.
“Tuni aka ci gaba da aikin lodin mai a yankunan da ba su da irin wannan matsalar da kuma wadanda aka shawo kan yadda za a kauce wa matsalolin, kuma muna fatan za a ci gaba da samun sauki wajen daida komai cikin kankanin lokacin,” Soneye ya shaida.
Soneye ya gargadi gidajen mai da cewa kada su yi ganganci da motoci ko rayukan mutane wajen yin jigila a yanayin da bai da kyau, domin guje wa abun da ka iya je ya dawo.
A wannan lokaci dai an samu karancin mai da kuma dogon layuka a gidajen mai a wasu sassan kasar nan, lamarin da ya janyo wahalhalu ga jama’a.