Mutane kan yi tambaya a kan abin da ke haifar da matsalar fitsari mai kumfa. Kafin sanin dalilin, ya kamata fahimci yadda fitsarin yake:
Fitsari ya kunshi wasu ‘yan kananan tarkacen kazanta, wadanda Koda (kidney) ke tacewa; sannan ta fitar da su daga cikin jini sakamakon ayyukan da jiki ke yi.
Kananan tarkacen kazantar da ke cikin fitsarin lafiyayen mutum sun hada da:
1- Ruwa kashi 95 cikin 100.
2- Sinadarin ‘urea’ 9.3 g/l.
3- Sinadarin ‘chloride’ 1.87 g/L.
4- Sinadarin ‘sodium’ 1.17 g/L.
- Sinadarin ‘potassium’ 0.75 g/L.
- Sinadarin ‘creatinine’ 0.67 g/L.
- Sinadarin ‘ammonia 30 micromole/L.
- Tarkace mai launin ruwan kwai, wanda ke samuwa ta hanyar lalacewar kwayoyin jini (pigmented products of blood breakdown).
Kazalika, idan mutum na da matsalar rashin lafiya; yawan sinadarin da aka lissafa a sama; zai kasance adadinsu ya fi haka ko kasa da haka a cikin fitsarinsa. Sannan kuma, za a iya samun karin sinadarai a cikin fitsarin nasa ko kuma yanayin fitsarin ya zama kamar haka:
1- Sinadarin ‘protein’ (proteinuria).
2- Sinadarin ‘glucose’ (sugar).
3- Kwayoyin jini (hematuria).
4- Rashin iya yin fitsari mai yawa (oliguria).
5- Yin fitsari mai yawan da ya wuce kima (polyuria).
6- Jin zafi lokacin yin fitsari (dysuria).
Abubuwan Da Ke Haddasa Fitsari Mai Kumfa (Causes of foramy urine):
Fitsari mai kumfa ya kasu gida biyu; akwai mai matsala, akwai kuma mara matsala.
Fitsari mara matsala na faruwa ne idan:
1- Mutum ya rike fitsarinsa na wani tsawon lokaci ba tare da ya je ya yi ba, alhali kuma ya matse shi.
2- Yayin da mutum ke sakin fitsarinsa yana fita da karfi sosai. Hakan zai sa a ga kamar kumfa na tashi; sakamakon karfin fitar fitsarin.
3- Yin fitsarin a wurin da aka wanke da sinadarin wanki (detergent) ko sabulu (soap) ko kuma sauran sinadarai masu kumfa na wanke bandaki. Ragowar kumfar sinadarin, idan ya hadu da fitsari, zai samar da kumfa ta yadda za a ga kamar fitsarin ne ke da kumfar.
- Ya kasance mutum ba ya shan ruwa sosai (dehydration), akwai yiwuwar fitsarinsa ya zama mai kauri (concentrated).
Hakan zai sa fitsarin nasa ya yi kumfa.
5- Daukar tsawon lokaci ana amfani da wasu magunguna na kashe radadi ko rage kumburi ko zazzabi (non-steroidal and ani-inflammatory drugs), kamar ibuprofen, diclofenac, naproden, indomethacin da sauran makamantansu, ya kan sa fitsari ya yi kumfa.
- Cin abinci mai zaki sosai (sugar), ko ‘protein’ zalla ba tare da an sirka shi ba, shi ma ya kan sa fitsari ya yi kumfa sosai.
Fitsari Mai Kumfa Wanda Ke Da Matsala
Wannan na faruwa ne sakamakon:
1- Ciwon siga (diabetes): Idan mutum na da ciwon siga, Kodarsa na shan wahala wajen tacewa da kuma hana siga da ‘protein’ din cikin jininsa daga shiga fitsarinsa. Da zarar sun shiga, fitsarinsa zai iya yin kumfa.
2- Ciwon Koda (kidney disease): ko da mutum ba shi da ciwon siga, idan yana da ciwon Koda, shi ma zai iya sa fitsarinsa ya yi kumfa.
3- Cutar mafitsara (urinary tract infection – UTI): Idan mutum yana da wannan cuta, kwayoyin cutar za su kasance a cikin fitsarinsa, don haka zai iya yin kumfa.
Yadda Za A Magance Yin Fitsari Mai Kumfa (Treatment of foamy urine)
Matakan da za a dauka wajen magance matsalar kumfar fitsari, ya danganta da abin da ya kawo ta. Idan ciwon siga ne ko hawan jini ko koda, sai a yi maganin wadannan cututtukan; domin fitsari ya koma daidai. Idan kuma rashin shan isasshen ruwa ne, sai a rika shan wadataccen ruwan kuma tsabtatacce akai-kai. Idan kuma yawan rike fitsari ne, sai a rika yin sa da zarar an ji ana bukatar yin sa.
Haka zalika, yana da kyau mutum ya dage wajen cin lafiyayye kuma wadataccen abinci tare da yawan motsa jiki, sannan kuma da kokarin kauce wa shan taba sigari ko giya.
Daga taskar Dakta Usman Hassan