Kwarin da ke shiga cikin gashin Akuyoyi da Tumaki suna cutar da su, na zama babbar barazana ga samun ingantattun Tumakin da kuma Akuyoyi, wanda hakan ke taimakawa wajen samun karancin ingantacciyar madara tare kuma da shafar lafiyarsu.
A saboda haka, ana bukatar mai kiwo ya kula sosai ta yadda zai kare dabbobinsa daga harin ire-iren wadannan kwari, don kula da lafiyarsu.
Bisa ci gaban da aka kara samu a fannin fasahar zamani, zai taimaka wa mai kiwon kwarai da gaske wajen amfani da fasahar, don kare dabbobinsa daga harbin wadannan kwari.
Kazalika, ta hanyar amfani da ingantattun magunguna da sauran kayan da ke kashe irin wadannan kwari da ke addabar dabbobi, hakan zai taimaka wajen kare dabbobin daga kamuwa da cututtukan da ke addabar su kai tsaye.
Tsutsar Da Ke Shiga Cikin Gashin Dabbobi:
Wannan Tsutsa na yi wa gashin Tumaki da Akuyoyi matukar illla, musamman a lokacin yanayin hunturu na sanyi. A nan, ana yi wa Gashin nasu feshe ne da magungunan da ke kashe Tsutsar.
Kwayoyin Cuta Daga Kudaje:
Wannan ma wata babbar annoba ce da ke yi wa Tumakai da Akuyoyi illa a cikinsu, don haka wajibi ne mai kiwon dabbobi ya tabbatar yana kokarin kare dabbobinsa daga harbuwa da wannan cuta.
Kwarin Da Ke Cinye Gashin Tumaki:
Ana bukatar duk wata Akuya ko Tunkiya da ta harbu da cuta daga ire-iren wadannan kwari, mai kiwo ya tabbata ya tuntubi kwarrun Likitocin dabbobi, don duba lafiyarsu tare kuma da killace su a wuri guda, duk kuwa da cewa; akasarin wadannan dobbi sun fi kamuwa da wannan cuta ne a yayin da suka fita yin kiwo.
Kwarkwatar Tumaki:
Babu wani abu mai wahala wajen yin feshi a Gashin Tumakin da ke dauke da Kwarkwata a jikinsu, ana kuma bukatar kafin mai kiwo ya sanya sauran dabbobinsa a cikin wani Garken dabbobi, ya yi kokarin duba lafiyarsu.
Kwaron Kaska:
Kaska na matukar cutar dabbobi, musamman Tumaki ta hanyar shiga cikin kunnuwansu tare da sanya kaikayi a jikinsu da kuma lalata Gashinsu baki-daya; idan har ba a yi saurin dakatar da ita ba.
Da duk lokacin da kwaron Kaska ya harbi Tumaki, za a iya yi wa Gashinsu nasu feshe, haka nan kuma; ana so a duk yayin da za a yi feshin a kula tare da kiyayewa sosai.
Daukar Matakan Kariya:
Ba a so a rika yi wa dabbobi feshi a matsattsen wuri ko kuma a wurin da iska ba ta samu tana shiga.
Haka zalika, ba a so a yi wa dabbobi wannan feshi; a lokacin da suke kan jin kishirwa ko yanayin zafi da ake bukatar su sha ruwan kafin a yi feshin, don gudun ka da su sha maganin feshin.
Ba a so a yi wannan feshi a lokacin da dabbobin ba su da lafiya ko kuma sun gaji.
Haka nan, ba a so a yi wa ‘ya’yan dobbobin feshi; yayin da suke kasa wata uku, ana kuma so a yi amfani da maganin feshi mara karfi. Kar ka yi wa dabbobin da suka harbu feshi da maganin feshin da ake kira a turance ‘coumaphos’ a cikin kwana goma, don gudun ka da su harbu da manyan kwayoyin cuta ko sauran cututtuka.
Sauran Wasu Matakan Da Ya Kamata Masu Kiwo Su Kiyaye:
Akwai wasu magungunan da ke amfani da su wadanda ake samun su a kasuwa, kamar Alluran da za su yaki ire-iren wadannan kwari da ke addabar Tumaki da Akuyoyi.
Wadannan magunguna su ne aka fi amincewa da su, sakamakon irin tasirin da suke da shi; yayin amfan da su.